Yan bindiga sun yi barazanar sace shugaban kasa Muhammad Buhari da kuma Gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i tare da kashe su
Kamar yadda Aminiya ta ruwaito Cewa ’Yan bindiga sun yi barazanar sace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a wani sabon bidiyo da suka fitar.
A sabon bidiyo da Aminiya ta gani, ’yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjoji sama da 60 a jirgin kasa da ke jigila tsakanin Abuja da Kaduna tun a ranar 28 ga watan Maris, sun yi barazanar sacewa da kashe Shugaba Buhari da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai