DA DUMI-DUMIN SA: ‘Yan ta’adda sun kai hari kan jami’an tsaron fadar shugaban kasa bayan barazanar sace Buhari.

0

Kamar yadda Jaridar The Nation ta wallafa ‘Yan ta’adda sun kai hari kan jami’an tsaron fadar shugaban kasa bayan barazanar sace Buhari.

 

Kimanin sa’o’i 24 da ‘yan ta’adda suka yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Kaduna Nasir El’Rufai a wani faifan bidiyo, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi wa sojojin na Guards Brigade kwanton bauna a Abuja.

 

Sojoji uku ne suka jikkata yayin harin wanda ya jefa mazauna birnin tarayya cikin firgici.

 

‘Yan bindigar sun nufi makarantar koyon shari’a ta Najeriya da ke Bwari a lokacin da suka ci karo da sojojin.

 

Akwai rahotannin sirri, kamar yadda majiyar sojoji ta bayyana, ‘yan ta’addan sun mamaye babban birnin tarayya Abuja da nufin kai hari a makarantar koyon aikin lauya da ke Bwari da wasu cibiyoyin gwamnati.

 

Majiyoyin soji da suka nemi a sakaya sunansu sun ce harin na nuni da cewa ‘yan ta’addan sun mamaye birnin amma hukumomi sun ce suna kan bin maharan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here