Gwamnatin Tarayya Ta Rufe FGC Kwali Saboda Barazanar Tsaro

0

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kwali da ke Karamar Hukumar Kwali a Babban Birnin Tarayya, Abuja ba tare da bata lokaci ba.

 

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayar da wannan umarni a wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar Ben Goong ya fitar ranar Litinin a Abuja.

 

Adamu ya ce rufewar ya zama dole ne biyo bayan wani ta’addancin da aka samu a kauyukan Sheda da Lambata da ke wajen karamar hukumar Kwali wanda kuma ke barazana ga FGC Kwali.

 

Adamu Adamu ya kuma bayar da umarnin a shirya yadda daliban shekarar karshe za su kammala jarrabawar kammala sakandare (SSCE) da hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO) ta shirya.

See also  PDP A KATSINA ZA TA CHANZA TSARIN YAKIN NEMAN ZABEN TA

 

Ministan ya umurci shugabannin kwalejojin Unity da ke fadin kasar nan da su hada kai da hukumomin tsaro da ke yankunansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here