Likkafar Matashi Honarabul Musa Gafai Na Kara Haskawa, Ya Zama Mataimakin Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaɓen Atiku A Jihar Katsina

Ganin Irin Rawar Da Hazikin Matashin Ɗin Siyasar Da Yake Takawa A Siyasar Jihar Katsina, Ƙungiyar Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa A Ƙarƙashin Jam’iyyar PDP Ta Atiku Haske Organization Ta Naɗa Honarabul Musa Gafai A Matsayin Mataimakin Shugabanta Na Jihar Katsina.

Bayanin Hakan Na Kunshe A Cikin Wata Takardar Amincewa Da Naɗin Nasa A Matsayin Mataimakin Shugaban Na Jihar Katsina Da Shugaban Kungiyar Na Jihar Katsina, Alhaji Bishir Babba Kaita Ya Sanya Wa Hannu.

A Tattaunawarsa Da Manema Labarai Bayan Mika Masa Takardar, Honarabul Musa Yusuf Gafai Ya Sha Alwashin Cigaba Da Bada Guddummuwarsa A Siyasance Don Ganin Ƴan Takarar Jam’iyyar PDP Sun Samu Nasarar Lashe Zaɓen Shekarar 2023 Idan Allah Ya Kaimu.

Honarabul Musa Gafai Wanda Shi Ne Darakta Janar Na Shahararriyar Kungiyar Nan Ta (Ladon Alkhairi) Wadda Ta Yi Fice Wajen Tallata Kudurorin Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Katsina A Ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Danmarke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here