TABBAS ALLAH YA ISA, LABARIN MAI TALLAR RAKE DA MAI MOTA.
daga Sani Rogo Aikawa kano.
Safiyar jiya Lahdi, misalin ƙarfe goma na safe wani mai mota yayi fatali da kayan tallan raken wani matashin dattijo, maimakon mai motar ya ba shi haƙuri sai ya ci magani yaƙi ya ce komai. Duk raken ya zube a kwata. Mai raken ya zo gaban mai motar ya ce, “Me yasa ka zubar mini da rake”? Mai motar ya kalleshi ya ce, ” Uban wa ya ce ka tare hanya”?
Mai rake ya ce, babu inda na tare hanya kai dai kawai ka zalunceni, kawai ka biyani. Nan da nan mai motar ya hau shi da zagi yana cewa anƙi a biya ɗin, cikin hawaye mai raken ya ce, bakasan wahalar da nasha na sami jarin ba, amman ka zubarmin ka cuceni ka cutar da rayuwata.
Mai motar ya ci gaba da zaginsa. Mai rake ya kalleshi ya ce, da ƙarfin ikon Allah sai ubangiji ya gaggauta yi mini sakayya. Allah Ya isa!! Allah Ya isa!! Allah Ya isa!!!
Sau uku yana faɗa, babu yadda banyi ba akan mai motar ya daina zaginsa sannan ya biya shi haƙƙinsa, amman sai ya haɗa har da ni yana zagi, muna ji muna gani mai motar yayi gaba abinsa bai biya shi komai ba ya tafi.
Mai rake ya ci gaba da zubarda hawaye. Tausayinsa ya kama ni sosai, sai na zaro kuɗi na biya kuɗin raken duka sannan na ƙara masa da wani abu. Wallahi sai naga yana kukan farin ciki a karo na biyu, yana ta yi mini addu’a, tare da cewar Ubangiji ya ninka maka fiye da abinda ka tallafa mini, nayi gaba na barshi yana ta addu’a.
Banfi minti uku ba daidai Tal’udu junction naci karo da wata tsohuwar ƙawata da mukayi FCE KANO da ita, munfi minti goma muna hirar yaushe gamo, da zamu rabu tace bari in baka kuɗin mai, wallahi sai da ta ninka mini abinda na baiwa mai raken nan sau 16 tare da wasu canji. Nan take sai addu’ar mai rake ta faɗo min da ya ce Ubangiji ya ninka maka fiye da abinda ka bani. A zuciyata nace tabbas Allah Ya isa!!!.
Bari kuji wani hukuncin Allah. Ko minti uku banyi ba, sai naga taron mutane akan titi anata zuwa dubawa, nima banyi ƙasa a guiwa ba sai na leƙa, iko sai Allah. Mai motar da ya buge mai rake ne kwance ana yi masa fifita gaban motar ya tashi daga aiki, hannunsa ya karye, wai ashe dukan wani bangon titi yayi shi kaɗai yayi accident.
Na sake kallonsa, ya shaida ni, na shaida shi. Na ce sannu Malam Allah ya kiyaye gaba. Tabbas Allah da isa Yake. Nayi gaba abina inata tunanin ƙudirar Ubangiji.
Yakamata muji tsoron Allah mu daina raina kalmar Allah ya isa.
Sani Rogo Aikawa