‘Ni yasa na nemo masa ‘yan matan da ya damfara’ -Abdulrazak Musaddiƙ

0

‘Ni yasa na nemo masa ‘yan matan da ya damfara’ -Abdulrazak Musaddiƙ-

 

A ranar Lahadi 26/6/2022 ne, wani matashi ya damfari’yan mata manyan wayoyin hannu sama da guda 60 a garin Malumfashi da ke cikin Jihar Katsina,wanda kuma tun daga ranar ya yi batan-dabo, babu shi, balabarinsa.

Domin jin hakikanin yadda lamarin ya faru, Wakilinmu ya zanta da Abdulrazak Musaddik, wanda shine matashin da dan damfara ya bai wa aikin tara masa matan da ya yi sama da fadi da wayoyin nasu. Ga abin da yake cewa: A ranar Asabar 25/6/2022 ina wurin sana’ata ta POS da sai da katin waya, sai mutumin ya zo shagona ya fitar da kudi ta POS.

Mutumin matashi ne yana sanye da Kananan kaya, yana sanye da riga mai dauke da tambarin kamfanin MTN da kuma hula fesin kaf, ita ma mai dauke da tambarin na kamfanin MTN.

Yana da kasumba, yana da cin zanzana a hakoransa, kuma yana da jan lebe. Yakuma zo ne a kasa ne, ba a kan abin hawa ba. “Bayan ya fitar da kudin sai ya ce min shi ma’aikacin MTN ne kamar yadda nake gani, ga ma ID Card (katin shaida) dinsa. Saboda haka ya za a yi a tara masa mata za a yi masu wani ‘program’ na kwanaki uku da an kammala za a biya su kudin aikinsu na ‘training (horaswa).

Sai na ce masa to babu matsala, insha Allahu za a samar da su. Bayan ya tafi ba da jimawa sosai ba, sai ya sake dawowa ya ce mani a tara su gobe Lahadi da safe za a fara. Na ce masa ba matsala.

Ya ba ni lambar wayarsa ya tafi Ashe da ya bar nan sai ya tafi kuma shagon daya daga cikin masu sana’ar daukar hoto a garin Malumfashi, wato NICE JOE, shi ma ya bukaci ya tara masa mata kamar yadda ya shaida mani, ya kuma ce shi Nice Joe din ne zai yi masu hotuna a wurin taron wadanda za a tura wa kamfani. “Da ni da wasu abokanina muka bazama wajen wayar da kai da kuma tattara matan da za su zo domin amfana da wannan shiri. “Da safiyar ranar Lahadi 26/6/2022 na tattaranmasa mata matasa guda 40, yayin da shi kuma NICE JOE ya tattara kimanin mata matasa guda 20.

Lokacin da dukkaninmu muka hallara a wurin gidan man Lolo Dakare. Da isowar mutumin sai muka dunguma muka tafi otel din Salamah Hotel da ke kan kwanar Kafur, inda ya ce ya kama wuri domin gudanar da taron.bBayan mun zauna a cikin otel din sai ya sanya aka kawo mana abinci daga gidan abinci na SAHAB RESTAURANT kimanin filet 70 da ruwan sha na cikin roba.

Bayan an ci an sha sai ya ce to za a yi kwalliya a fuska ta kamfanin MTN, za a kuma sanya riguna na MTN, sannan a dauki hotuna. Akwai wadansu mata guda biyu da ya kira daga Kano wadanda sune masu yin kwalliyar, sai kuma ya hada da daya daga cikin jama’ar da NICE JOE din ya zo da su, a inda masu yin kwalliyar suka zama su uku ke nan.

Bayan an yi kwalliyar sai ya nuna wani daki yace kowace ta je ta ajiye wayarta da jakarta a wurin saboda ba zai yiwu a yi hoton ana rike da jaka ko wayoyin hannu ba. Kowa sai ya shiga ya ajiye wayarsa, in ban da wata da ta ce ita gaskiya ba za ta ajiye wayarta ba a inda ya ce to lallai kuwa korar ta zai yi. Ba za a yi program’ dn da ita ba matukar ba ta ajiye wayarta ba. Bayan an ajiye wayoyin sai ya sanya a shiga layi domin shirin daukar hoto da kuma fara gabatar da program’.

A yayin da aka shiga layin sai daya daga cikin yan tsirarun matasa maza da ke wurin ya ciro wayarsa daga cikin aljihu da nufin daukar hoto, sai mutumin ya ce masa kai ya aka yi ba ka ajiye wayarka ba? Sai ya ce masa

 

Ba ya so a dauki hoto da waya, domin kar a dora a social media, tun da akwai wanda aka tanada domin ya dauki hoton da za a tura wa kamfani. Don haka ya kawo wayar tasa a ajiye. Sai ya ce ai wayar ba ta da caji sosai caji ma zai sa. Sai ya ce to ya kawo ya sanya masa cajin. Sai ya ba shi

 

wayar kirar iPhone sabuwa, har da ma cazar domin ya sanya masa caji kamar yadda ya ce.

 

“Da ya karba sai ya ce mana, yana zuwa yanzu, da ya fita daga inda muke din sai muka ji shiru bai dawoba. Don haka sai na kira lambar wayarsa sai ya daga ya ce mani yana zuwa yanzu ya je su taho da wasu kayan aiki ne. “Da muka ji shiru dai zuwa wani lokaci mai tsawo bai dawo ba, sai na sake kiran layin wayar tashi sai naji ta a kashe. Danaji haka kawai sai muka fito daga inda muke, sai muka ga ashe ya shiga dakin nan ne da aka ajiye wayoyi ya kwashe wayoyin duka ya tafi da su. Daga nan kuma ba a sake kiran layin wayar tashi ta shiga ba. “Da muka ga haka sai muka fito daga otel din gaba dayanmu muka dunguma zuwa ofishin Area Commander da ke daura da wurin da lamarin ya faru, inda muka bayyana wa jami’an ‘yan sanda abin da ya faru, aka kuma rubuta bayaninmu, aka ce mu je mu saurara za a bincika, lamarin da har yanzu shiru ba a neme mu aka ce mana komai ba, inji Abdulrazak Musaddik.

 

Ya kara da cewa; “Lallai ya tafi da wayoyi sama da guda 50, domin kuwa akwai wadanda suke da wayoyi guda biyu, babba da karama, kuma duka ya tafi da su.

 

Kuma akwai manyan wayoyi wadanda kimar kudinsu ta haura Naira dubu 100 da daman gaske a cikin wayoyin. Da yake amsa wata tambayar dangane da sunan mutumin da kuma yadda ta kasance tsakaninsa da sauran matasan da aka damfara wayoyinsu kasantuwar shi ne yazama silar haduwarsu da mutumin? Sai ya ce, ” Lallai ban san sunansa ba, saboda bai fadi mana sunansa ba, lambar wayarsa kawai ya ba ni, kuma tun daga lokacin har ya zuwa yanzu ba ta kara shiga ba.

Duk lokacin da aka kira wayar a kashe ake jin ta. Kuma su mutanen sun fahimci cewa ni ma yaudarata ya yi, kuma ba ni kadai ya yaudara ba, domin kuwa hatta masu gidan abincin da muka ci wanda ya sa aka kawo daga SAHAB da ke jikin ginin otel din, su ma bai ba su kudin abincin ba. Hakan nan kuma shi ma man fetir din da aka karbo aka sanya a jannareton da aka kunna a otal din, shi ma bai biya kudin ba. Hatta su ma otel din bai biya su duka kudinsu ba, kuma har da wayoyin masu kwalliyar da ya kira da kansa daga Kano ya hada ya tafi”, Abdulrazak Musaddik, ya bayyana.

 

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahotan da babu amon wannan dan damfara, kuma shiru. Jami an yannsanda su ma ba su nemi wadannan matasa da wannan azalnta fada masu ba domin su yi masu wani karin bayani dangane da lamarin. Daga Jaridar Almizan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here