ASALIN TA “ADDANCI A “YANKARA , KEWAYE DA HALIN DA AKE CIKI YANZU.

0

Awwal jibrin

@ katsina city news

‘Yankara ta karamar hukumar faskari jahar katsina,na daya daga cikin garuruwan da yan’ta’addar daji suka lahanta, kasantuwar garin na da kasar noma da ma’adanai, dake a karamar hukumar Faskarin jihar Katsina, Kuma ya yi iyaka da jihar Zamfara daga Yamma.

Baya da nisa da dajin da yayi iyaka da jahar Kaduna, kebbi da sokoto.

Da yake shai’dawa Jaridun Katsina City News, ya bayyana tun a wajajen shekarar 2019 aka fara samun gamayyar wasu bata gari tsakanin kabilun Hausawa da Fulani, su na tare hanya, su na fashi da Mashina da Wayoyi da raunata mutane.

 

Abin ya kara ta’azzara a wajajen karshen shekarar ta 2019, gaiwa ta fara cin ‘yar’uwarta inda wasu Fulani Dazukan Garuruwan Madani da Yanfa Rigar Mai Islamiyya da sauransu, suka fara amshe Shanun Junansu, inda suke kai farmaki a ruga ko wuraren kiwon suna amshe Dabbobi.

 

Wannan ne ya haifar da kafuwar kungiyoyin amsar Dabbobi a tsakanin Fulani da sunan Daba, duk gidan Fulani za a samu mutum a cikin dabar inda aka ki kuwa za a yashe Dabbobin su, ko a rikicin da zai haifar da salwantar rai.

 

Suna Kara ta’addancin suna Kara karfi, domin bayan shanunsu sun karanci ta hanyar kwata a sayar, sai suka far shigowa kauyuka amsar Dabbobi, inda aka samu turjiya su Bude wuta, ta haka suka addabi yankin manoman yankin suka rasa Shanun Huda.

 

Haka aka yi ta zaman kila wa kala a tsakanin al’ummar yankin, a shigowar azumin watan Ramada na shekarar 2020, inda abin ya Fi ta’azzara.

 

Domin a ranar Alhamis din karshen watan suka farmaki wasu Matasa uku a Rafin Gabas dake garin ‘Yankara, wadanda suka je tafkin domin wanka, suka kashe biyu dayan ya tsira da harbi.

 

Wannan ya fusata al’ummar garin, domin sun san masu yi masu ta’addancin don haka suka dauki mataki.

 

Inda a ranar juma’a sai ga mahaifiyar ‘ya’yan dabar da suka kashe yaran, wadda ake kira da Abu, ta shigo garin na ‘Yankara, wajajen 11:00 na safe, domin dama ta taba fadar ‘Yankara ta gama zama lafiya, don haka wasu Matasa biyu da ake zargin ‘Yansakai ne suka farmake ta, daga masallacin juma’a, zuwa bayan gari Mangwarorin Birnin ruwa suka sassarata, nan take ta ce ga garinku ne.

 

Labari ya karade garin an kashe, Abu. Ba a yi aune ba, sai aka ringajin karar harbi daga yaranta, inda suka zo domin daukar gawar Mahaifiyar su. Daga bisani suka Aiko da sakon a Jira dawowarsu.

 

Bayan kamar awa da daukar gawar wato, misalin 12:30 na rana, aka ringa Jin Harbinkan Mai uwa da wani, an tunkaro garin na ‘Yankara, inda aka yi dauki ba dadi tsakani jami’an Yansanda da Yansaika, suka mayar da martani, sai dai tilas jami’an suka juya domin an fi su kayan aiki, inda ‘yanta’addar suka biyo su har cikin gari.

 

Kazalika, ‘yanta’addar sun Kara yo shiri da gayyato wasu Dabobin yanfashin dajin, suma yansaika da jami’an Tsaro suka Kara shiri da neman dauki. Wajajen karfe 4:00 na yamma suka tukari mazaunin ‘Yan’ta’addar dake a garin Madani, rashin sani ya Sanya aka yi wa jami’an kwanton Bauna a saman bishiyoyi da Ramuka, ana matsar su suka fara ruwan harsasai, dole jami’an tsaron suka juyo baya neman ceton rai. Su Kuma ‘Yandabar suka dafo masu baya inda suka kashe jama’ar garin da dama, har wa yau da daddare suka bi gida gida na ‘Yansakai suna kashe Wanda suka tarar da wasu Shagunan da bannata dukiyoyi.

 

Tun daga ranan suka Sha alwashin duk juma’a sai sun farmaki garin, wannan shi ne asalin rikicin ‘Yankara da ‘Yan’ta’addar Daji.

 

Nadin kasurgumin danfashin dajin Adamu Aleru, ya zama tamkar kofar sasanci ga al’ummar yankin, domin al’ummar ‘Yankara sun tura masa wakilai, domin yin sasanci da neman hana yaransa kai masu farmaki, a zauna ba cuta ba cutarwa a tsakanin al’umma, in ma wasu sun zo yi masu zai hana.

 

Duk da wannan sasanci ana biyan kudin kasa, dun daga suka da noma da cira kowane sai an biya kudi, domin gudun kisa, duk harkokin noma an tayar Mai da sasanci, sai an biya haraji.

 

Yau da kullum ta sanya mazauna yankunan lakantar yanayin da ake kawo masu hari, domin su kan yi tsare tsare, na rufe fuskoki da nikabi ko hijabi ko kuma kai tsaye. Sannan kuma, in za su shigo gari, basu haduwa su shigo tare, su na rabuwa ne shiyya shiyya, sannan kuma akwai wanda zai fara harbi.

 

Ko a harbin akwai na inkiya da a dakata an yi nasara, don da an ji shi za su saurara su kama hanyar fita, domin an gama. Haka ma, idan suka zo daukar mutum suka zo da salon Kewaye unguwar da yake, sannan bada harbi, sai sun tabbatar sun dauki Wanda suka zo daukar, bayan sun dauka, sukan Kara daukar wanda ya tare masu gaba domin garkuwa dasu.

 

Duk da haka, bayan an yi sasanci, a ‘Yankara, a wajajen farkon shekarar 2020 da aka cire amfanin gona. An dauki tsawon lokaci, al’umma sumar yankin walwala da sakon rai da hulda, Amma duk da haka an dardar, domin masu aika aikar sukan shigo gari ba makamai su yi huldodinsu cikin al’umma, kamar yadda aka Saba.

 

Har zuwa samun Sarautar Sarkin Fulanin Dajin ‘Yandoto, Wanda nadin ya wanzu a masarautar ‘Yandoto a ranar 16/7/2022, inda aka nada Adamu Aleru Yankuzo, a matsayin Sarkin Fulanin Yandoto.

 

Al’ummar yankin sun yi murna da karin karfin da ya samu, don haka suka rinka jinjina da biyaya domin an daina Kai masu farmaki. Kwatsam, kwana daya da nadin, wato ranar Lahadi 17/07/2022, Gwamnatin jihar Zamfara ta tsige Adamu Aleru daga kan Sarauta Sarkin Fulanin Daji tare da wanda ya nada shi, Sarkin Yandoto.

 

Sai Kuma ga kakakin rundunar Yansanda na jihar katsina, Acp Gambo Isah da kuma Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, sun fito sun shaidawa manema Labarai, har yanzu suna neman Adamu Aleru ruwa jallo, a Raye ko a mace.

 

Duk da al’ummar yankin sun nuna wa gwamnatin ya tuba, Amma sun nuna ko ya bari ba sasanci sai an bi Kadin jinanan da ya salwantar a garin Kadisau da Yankin Faskari.

 

Wannan batu na Hukuma, ya Sanya mutanan Adamu Aleru suka fara kai farmaki kan hanyoyin da Kauyukan Yankin tare da shigowa Garuruwan Faskari da Yankara da Kwakware da Sheme da Unguwar Ali da sauransu.

 

Ko baya ga haka, yan’ta’addar sun ci gaba da bin manoma gona, suna kwace masu Dabbobi tare da kashe su, kamar da suka Saba. A Yankara sun kashe Hamida Kogawa da kure masa Shanun hudu, bayan sun kashe shi, wanshekare matarsa ta haifi da namiji.

 

Ko a garin Ruwan Godiya, sun kashe mutum hudu kan hanyar Sheme zuwa Kankara ma, sun kashe Yansanda Mopol guda biyar tare da arcewa da Bindigoginsu.

 

A kididdigar da aka fitar a cikin kwana biyar da dakatar da nadin kasurgumin danfashin dajin Adamu Aleru, an kashe sama da mutum 50 da asarar dumbin miliyoyi da dukiya.

 

Duba da haka ne, al’ummomin yankin suka Kara shirya zama domin sasanci da yin sulhu a Lahadi 24/7/2020, inda aka nemi Adamu Aleru kan suna barar a yi sulhu da kuma bayar da hakuri da nuna rashin Jindadin su na cire shi daga Sarauta, da nuna masa laifin gwamnatin basu talakawa ba.

 

An yi nasara ya amshi tayin, a zaman da aka yi shi a cikin mayakansa, da Mutanan gari, Wanda ya kusan shafe awa Daya, ana tattaunawa, inda aka yi sasanci kowa ya tafi cikin walwala da annashuwa, kamar yadda aka Saba a baya. Ana fatan wannan ya zama sauki ga al’ummar jihar Zamfara da Katsina.

Awwal jibrin Dan jarida ne daga aiki da jaridu daban daban harda Al mizan. Ya rubuto wannan Rahoton ne Musamman don katsina city news.

Katsina city news

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

@www.taskarlabarai.com

The links news

@ www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here