Yadda Ake Amfani da Fitsarin Mutane a Matsayin Taki

0

Daga Bashir Suleman

@ katsina city news

Kasar Malawi na daga cikin kasashe da suke bai wa noma muhimmanci, duba da yadda kasar ta samu kanta a cikin yanayi matsin tattalin arziki.

 

Wannan ta haifar da tunanin mayar da Fitsarin bil’adama takin amfani ga tsiran da ake nomawa.

 

A zantawar wani manona da da gidan talabijin na kasar chaina

ya bayyay yadda ya ke ganin sauyi da habbaka tsiran da yake nomawa a lambun bayan gidan, inda Fitsarin da suke ya ke kwarara a cikinsa.

 

Magidanci ya fara dakon rubobin a wajajen taruwar jama’a, suna Tara masa Fitsari, kana ya tace ya zuba sunadaran da zasu rage wari da kashe kwayoyin cutar da ke ciki. Ya kara da cewa da yana samu a kyauta daga bisani sai ya biya a wajajen masu kula da makewayi da jama’a ke zagayawa, inda yakan sayi jarkar Olga a kan 1500 da kudin Malawi ya sayar 5000.

 

Wasu manona da aka zanta da su, sun nuna gamsuwar su wajen wannan nau’in Taki Wanda kan haifar da yabanya Mai kyau a cikin kankanin lokaci, Wanda amfani da takin ya game ko’ina yankunan kasar.

 

Gaskiyar Hausawa da kan cewa ruwa na kasa, sai dai in ba a tuna ba.

Mun dauko labarin daga tashar talabijin ta kasar chaina mai CCGN.

an watsa rahoton a ranakun 17 da 19 ga watan February na 2022

Katsina city news

Www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

Www.jaridartaskarlabarai.com

The links news

Www.thelinksnews.com

07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here