Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne sun kai hari a wani shingen binciken sojoji da ke gindin shahararren dutsen Zuma Rock a jihar Neja a daren Alhamis.
Inda aka kai harin na da nisan kilomita biyu zuwa Zuba a babban birnin tarayya Abuja.
A cewar wata kungiyar tsaro ta Eons Intelligence a shafinta na Twitter, @eonsintelligenc, ta ce ‘yan bindiga da sojoji sun yi artabu da yan bindiga a shingen binciken ababan hawa da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna.
Ta rubuta Kamar haha: “A yanzu haka ‘yan bindiga da sojoji sun yi artabu a shingen bincike da ke Zuma Rock Madalla, daura da babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja. Yanzu haka dai jami’an tsaro na ci gaba da bin sawun ‘yan fashin…
A halin da ake ciki dai, wasu da suka shaida da lamarin sun bayyana yadda lamarin ya faru a shafukan su na sada zumunta. kamar dai yadda Jaridar Daily Trust Ta Wallafa A Shafin Ta