GOBARA TA KAMA WANI KEYUS DAKE JIKIN GIDAN MAN DAN MARNA KOFAR KAURA. 

0

@ katsina city news

Gobara ta kama wani keyus na gyaran waya da chaji dake kusa da masallacin gidan Mai na Dan marna dake kofar kaura cikin katsina.

Gobarar ta faru ne, sakamakon kawo wutar lantarki ta NEPA da karfin gaske da misalin karfe shidda na yammacin asabar 30/7/2022.

Shagon Mallakin wani mai suna Babangida wanda ya kusa shekaru ashirin yana sana a a wajen.

Babangida ya bar shagon nashi da mintuna kadan gobarar ta kama.mutane da yawa suka taimaka wutar ta ki fantsama zuwa ginin massalcin da shiga gidan man da benen dake kusa da gidan man. zuwan yan motar kashe gobara ya kammala kashe wutar.

A shagon akwai wayoyin mutane na gyara da kuma na chaji masu yawan gaske.sannan tsaffin wayoyi da kayan waya na saidawa.janareto dake cikin shagon kuma da fetur a ciki ya Sanya wutar ta rika Ruri.

Babangida mutum ne,mai Kwazon gaske.da rike sana arsa da Amana ga duk Wanda yasan shi.

Kwanan nan ya Sanya ma “ya “yansa mata bukin aure cikin watan Maulud ga kuma jarabawar da Allah ya jarabce shi da ita.

See also  AN DAKATAR DA DALIBAR DA TA KALUBALANCI GWAMNATIN JIHAR NASARAWA

Gidan Dan marna dake kofar kaura. tun daga aka Gina shi,ya kyale duk masu kananan sana o i, suka ci gaba da gudanarwa a kusa dashi ba tare da takurawa ba.

Wasu keyus, wasu dabbino, wasu gwanjo da masu kayan marmari a keken Baro duk suna sana arsu.

Wasu suna samun tallafin Alhaji Dahiru sarki mai gidan man duk shekara lokacin fitar da zakka.wanda wannan na taimaka masu kara bunkasa sana ar tasu.

Sai lokacin aikin Gadar kasa da aka fara,duk suka tashi.gwamnati kuma ta biya su diyyar tayar dasu dai dai gwargwadon sana ar kowa.

Babangida, shi kai ne, ke bai tashi ba.don aikin, bai shafi inda yake sana a ba.

Sai yanzu Allah ya kawo masa tasa jarabawar.

Katsina city news

Www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

Www.jaridartaskarlabarai.com

The links news

Www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here