ALERU YA KWATO MA MUTANEN YANKARA SHANUN SU.
Daga Auwal yankara
@ katsina city news
Ga alama sulhun da akayi tsakanin mutanen yankara ta karamar hukumar faskari ta jahar katsina da babban barawon dajin nan na jahar zamfara ya fara aiki.don kuwa.
A ranar Asabar 30/7/2022 wajen misalin karfe 8 na safe, wasu ‘Yanbindigar Daji su ka yi awan gaba da wasu Shanun, Alhaji Umaru Salisu, daya daga cikin limaman garin ‘Yankara.
Lamarin ya auku ne a gabacin garin na ‘Yankara, inda Kanen Alhaji Umaru suka je huda, suna cikin yin hudar ‘yanbindigar suka afka masu suka kwace Shanun.
Su na ji suna gani tilas ‘yanbindigar suka kora Shanun, su kuma suka dawo gida, ganin miyagun Bindigogin da suke dauke da su. Haka labarin ya ci gaba da wanzuwa na kwantar Shanun a cikin garin.
Ganin abin da ya faru, sai jagoran garin na ‘Yankara ya Kira shugaban ‘Yanbindigar Daji, Adamu Aleru, don shaida masa halin da ake ciki, na karbe masu shanu.
Inda nan take ya tayar da Kwamandojinsa dake Kewaye dashi yace su bi sawu.inda suka suka kwato shanun daga barayin da suka sace su.
Labarin da Majiyar jaridun katsina city news ke samu an mayar wa da Mai Shanun, shanunsa yanzu, Kuma jama’ar gari sun ci gaba da shiga Daji Dan gudanar da aikin su, biyo bayan sawowar Shanun.
A kwanakin baya ne, mutanen yankara suka gayyaci adamu aleru domin zaman sulhu dashi kuma yayi masu alkawalin zai tsare masu gonakin su su cigaba na nomar har zuwa kwasar amfanin gona.
Kuma har zuwa yau bai Saba alkawalin ba.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
@katsinacitynews.com
@ Jaridartaskarlabarai.com
@ thelinksnews.com