ILLOLIN SHAGWABA ‘YA’YA

0

Kalmar sangarta tana nufın duk wani abinda da ko ‘ya suka yi wanda bai dace ba, ba za a yi masu fada ba domin gudun kada zuciyarsu ta baci,duk wani abinda irinsu suka yi sai ace daidai ne ba wata matsala.

 

Abu na biyu kuma shi ne duk wani abinda suka son a yi masu daya jibanci kudin nan da nan za ayi masu, ko kuima a basu ahaka za a basu.Sai dai kuma wani abu sannu a hankali idan har aka cigaba da irin wannan hali na sangarta ya ya, su zama yan lele ba a son tada masu duk wani abinda zai bata masu rai.

 

Yau da gabe sai Allah domin kuwa babu wani abinda ke dauwama sai ikon Allah,komai na iya sauyawa ba tai fadawa mutum 2a a yi ba cewa ga lokacin da al’amarin zai kasance ba.Wasu sai a bata su da kullum jin dadi ba tare da nuna masu hanyoyin da ake samun

kudin ba,ba a koya masu sana’ a, zuwa makaranta ma ba a matsa masu su je.

See also  Tinubu Ya Shiga Tsakani Kan Yunkurin Tsige Gwamnan Jihar Ribas

 

Har da idan ta Allah ta kasance ko sauyawar rayuwar kamar yadda na riga na yi bayani ido ya fara raina fata.

 

Ko dai na gaba ya koma baya wanda daga haka ne abubuwa ske sauyawa ga wadanda aka kwadaitawa kullum dadi sai kashe kudi.Ba a san yadda za a nemo su ba amma an san hanyarr kashewa, tun da dai an saba da dadin

daga wahala ta shigo, dole ne a shiga aikata

abubuwan da basu dace ba, domin dai kawai aji dadi.

 

Irin wadannan ya’yan da aka sangarta daga karshe da idan ba saa ce aka yi abinda ba a so ne ya kan faru na aiakata abubuwan da basu

dace, wanda kuma a lokacin wankin Hula ya kai dare babu wani gyaran da za a yi, domin kuwa icce ya kai ga rike wa ya yi girma, idan aka yi kokarin yin wani abu karaya shi za a yi.

Majiya: Leadership Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here