DAGA Datti Assalafiy
Tun jiya na ga masoyan Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari suna yada wannan hoton tare da bayyana sakon cewa kotu ta bayar da belin Oga Abba Kyari, mutane da yawa suna ta kirana akan wannan labari mai dadi da suka karanta
Abinda ya tabbata shine har yanzu Kotu ba ta bada belin Sarkin Yaki ba, wannan hoton an daukeshi tun da jimawa, daya ne daga cikin Lauyoyin Abba Kyari ya dauki hoton tare da shi
Kuma Lauyan Abba Kyari ya dauki hoton ne a cikin Kotu, bayan ya isar masa da sakonku, wato ku masoyan Sarkin Yaki da a kullun kuke masa addu’ah da fatan alheri akan wannan jarrabawa da ta sameshi
Ku kwana da sanin cewa duk sakon da kuke yadawa akan Oga Lauyansa yana sanar dashi, sannan muma muna yin screenshot muna adana komai har zuwa ranar da Oga zai samu ‘yanci mu nuna masa
A madadin Sarkin Yaki da iyalansa da abokan aikinsa masoya, muna mika sakon godiya gareku bayin Allah, kuma muna neman alfarma ku cigaba da yiwa Sarkin Yaki addu’ah akan Allah Ya bashi ikon cin wannan jarrabawa
Insha Allah ranar 30 ga wannan wata August kotu zata yanke hukunci akan bukatar bada belin DCP Abba Kyari
Muna fatan Allah Ya fito mana da Sarkin Yaki lafiya Amin
Source: Dokin Karfe TV