Kotu Ta Tasa Keyar Wani Dan Wasan Kwaikwayo Na Bogi Tare Da Wasu Mutane Biyar gidan Gyaran Hali A Benin

0

Mai shari’a Efe Ikponmwonba na babbar kotun jihar Edo dake zama a Benin ranar Litinin, 1 ga watan Agusta, 2022 ya yanke wa wasu mutane shida hukuncin zaman gidan gyaran hali.

 

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Emejom Jude Chinomso, Okolie Collins, Hezekiah Oghenekume, Musa Dauda, Akinselure Adebayo da Obafemi Oluwatosin.

 

Hukumar EFCC shiyyar Benin ce ta gurfanar da su akan tuhuma daban daban masu alaka da sojin gona da yunkurin zambatar mutane.

 

Sun amsa laifukan da ake tuhumar su dashi.

 

Mai shari’ar ya yanke wa Collins da Chinonso hukuncin shekaru biyu ko su biya tarar Naira dubu dari biyu da hamsin da Naira dubu dari uku. Haka Adebayo da Dauda za suyi shekara daya ko su biya tarar Naira Dubu Dari da hamsin ko wannen su.

 

Mai shari’ar ya yanke wa Oghenekume hukuncin shekaru biyu ko ya biya tarar Naira dubu dari da hamsin

Source: EFCC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here