Katsina a cikin fargaba: Masu garkuwa da mutane sun sake shiga Unguwar Shola…

0

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News ?️

 

Rahotanni da muka samu na cewa mahara sun shiga Unguwar Shola Quarters a daren jiya Asabar, inda suka yi harbe-harbe, da jikkata da dama daga cikin su. Kuma ana saran sun tafi da wasu mazauna Unguwar.

 

Ƙasa ga kwana hamsin ɓarayin sun taɓa shiga Unguwar inda suka kwashi mutane sukayi garkuwa da su.

 

A ɗan tsakaninnan masu garkuwa da mutanen sun matsawa wasu yankunan kusa da Birnin Katsina, inda a cikin kwanaki biyu suka kai hari a ƙauyen dake bayan barikin Sojoji na katsina suka sace Mutane suka tafi babu wata turjiya, haka kuma Ɓarayin suka riƙa karakaina a ƙauyen Ɗan Tsauni dake a hanyar Babbar Ruga bisa Titin Batsari suka kashe Mutane suka kore Dabbobi tare da tafiya da wasu Mutanen.

See also  AN KAI HARI BATSARI TA JAHAR KATSINA

 

Unguwar Shola Quarters tana Yammacin garin Katsina bayan Babbar Asibitin koyarwa ta Gwamnatin Tarayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here