@ katsina city news
Shugabannin jam iyyar SDP na jahar katsina sun bayyana cewa, sun fito ne domin kwato da Ceto talakawa daga halin da suke ciki a jahar katsina da kasar mu baki daya.
Shugabannin sunyi wannan jawabin ne, a taron Manema labarai da suka Kira karkashin shugaban su na jaha.Alhaji Bello da sakataren ta na jaha Mustafa kurfi.
Taron Wanda aka gudanar dashi a gidan Dakta Usman Bugaje dake katsina.
Shugabannin sun bayyana cewa, jam iyyar SDP ta yi zaben shugabannin ta.kuma ta samar da yan takarkarin ta, a matakin gwamna.wanda Ibrahim zakari Ibrahim shine Dan takarar su na gwamnan katsina.sannan suna da yan takarkarin majalisar jaha har Goma sha takwas.da na majalisar tarayya.
Shugabannin na SDP suka ce,sun fito ne don juyayi da tausayawa Akan halin da jaha da kuma kasar nan ke a ciki.
Shugabannin suka ce, kishi da damuwar halin da kasa da jaha ke ciki ya Sanya suka shigo siyasar gadan gadan.wadanda Dukkanin su tsaffin yan ma aikatan kungiyoyin masu zaman kansu ne.
Shugabannin sun ce Sam basu gamsu da matakan da ake dauka ba na matsalar tsaro da jaha da kasa ke fuskanta.
Shugabannin sun ce akai akai zasu rika bayyana ma matsayar su akan halin da jaha da kuma kasar ke a ciki.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Email. Katsinacitynews2@gmail.com