Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kara Jaddada rashin shakku gurin yin Allah wadai, da kai farmaki kan baki da Hukumomin Jami’an tsaro a yankin kudu maso Gabas, dakuma Alkawarin kammala dukkan wani shirin na Daukan mataki binciko wadan da ke kitsa harin don gurfanar dasu a gaban kuliya cikin gaggawa.
Matakin na Shugaba Buhari na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu rahoto aikata kisan gilla wa wasu Ƴan Kasar mutum Shida, da kuma kisan rashin imani na Jami’an Ƴan Sanda a Sa’ilin da suke bakin aiki, Shugaban ya bukaci Al’umma da Shugabannin Addini kan su ja hankali kan kashe kashe, su tashi domin dabba ka kadon koyaswar Addinai da Al’adu.
“Wadan da ke da masani ya akan mutane da suka aikata wannan aiki su nuna su.”
Ya bayyana kokarin gwamnatin sa, kan tsaro da daidaiton Al’amura a yankin kudu maso gabas da daukacin Ƙasa baki daya, Shugaban yace dukkan wani rahoto na kashe kashe ako daga ina abin bakin ciki ne da ba za’a lamunta ba.
Shugaban ya mika sakon Ta’aziyya ga iyalan Jami’an tsaro da aka kashe dama kuma Gwamnati da Al’umman Jamhuriyar Nijar wanda maharan suka kashe Ƴan Kasar su.
Mal. Garba Shehu: Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a.
source: Buhari Sallau