Wani Mutum Ya Auri Kanwarsa, Ya Haifi ‘Ya’ya Hudu Da Ita

0

Wasu ma’aurata da aka bayyana sunayensu Paulin da Dorica sun bayyana a wata hira da suka yi cewa su ‘yan’uwa ne. Sun kuma bayyana cewa suna sane da alakar da suke da ita amma sun yi aure kamar yadda Hamada Blog ta wallafa

Wani Mutum Ya Auri Kanwarsa, Ya Haifi ‘Ya’ya Hudu Da Ita
Wani Mutum Ya Auri Kanwarsa, Ya Haifi ‘Ya’ya Hudu Da Ita

Paulin, wani mutum mai shekaru 28 ya bayyana cewa shi da ‘yar uwarsa, Dorica sun rabu da iyayensu a lokacin yakin da ya faru a Bunia, Congo lokacin da suke yara.

Dukansu sun tsere zuwa Miti ba tare da iyayensu ko danginsu ba.

Lokacin da yakin ya ƙare, Paulin ya bayyana cewa ya koma Bunia don neman iyayensu amma bai iya samun wata alama ta su ko wani dangin su ba.

Bayan neman iyayensu da basuyi nasarar ganin su ba, Paulin ya yanke shawarar fuskantar gaskiya kuma ya koma Miti don ya kasance tare da ‘yar uwarsa.

‘Yan’uwan sun kasance cikin ɓacin rai bayan da ba a gano asalin iyayensu ba, dalilin da ya sa Paulin ya yanke shawarar da su auri juna shi da ƙanwarsa.

Dalilinsa na yanke wannan shawara mai ban mamaki shi ne, zai taimaka musu su habbaka zuriyarsu tun da ana tsammanin su ne kawai waɗanda suka tsira.

‘Yar uwar tasa ta bayyana cewa ta kwashe kwanaki tana tunanin hakan kafin daga bisani ta amince da hakan kuma suka yi aure.

Suna zaune tare tun a lokacin dasuka haifi yaransu hudu daga dangantakar su.

Ma’auratan sun kuma bayyana a fili cewa za su ci gaba da zama tare, kuma ba za su yi nadama ba a kan ayyukansu da kuma shawarar da suka yanke.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here