@ katsina city news
Dan majalisar dokoki mai wakiltar Karamar hukumar Batsari, Alhaji Jabiru Yau Yau yayi Kira ga gwamnatin APC da kuma uwar jam iyyar ta kasa da dau matakin gyara da karatun tanatsu Kafin lokaci ya kure.
Dan majalisar yayi wannan bayanin ne, a taron Manema labarai da ya kai a ofishin yan jaridu masu aikawa da Rahotonni dake titin IBB katsina.
Dan majalisar yace, Rashin adalci shine tushen komi.yace irin halin da APC ke ciki shine ya taba samun jam iyyar PDP a zaben 2015.
Dan majalisar ya kara da cewa.yanzu a jahar katsina sanata ya fita da APC ya koma PDP , yan majalisun Tarayya bakwai sun fice daga APC haka ma wasu yan majalisun jaha.
Yace wannan yanayin abin tsoro ne, kuma,ya Kamata,jam iyya da gwamnatin APC su shiga taitayinsu.
Jabiru yau yau yace,Rashin Adalcin da akayi masa wajen zaben fitar da Dan takara.jam iyya a jaha bata dau wani mataki ba,don haka suna a kotun tarayya.
Shafin Facebook na jaridun taskar labarai da katsina city news zasu saka cikakkiyar hirar a shafukan su.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Email:katsinacitynews2@gmail.com