YADDA AKA KASHE DAN TA’ADDA ALHAJI ABDULKARIM 

0

Mu’azu Hassan

@Jaridar Taskar Labarai

 

Wani bincike da jaridun Taskar Labarai suka yi, sun gano hadin gwiwar jama’in tsaro uku ya kawo nasarar halaka babban dan ta’addar nan na yankin Safana ta Jihar Katsina, Alhaji Abdulkarim.

 

Bincikenmu ya gano Alhaji Abdulkarim yana daga cikin barayin daji biyar da suka jagoranci ‘yan ta’ addar da suka kai hari ga tawagar motocin shugaban kasa a watan Yunin da ya gabata.

 

Abdulkarim mai shekaru 35, yana da sansani ne a dajin Marina da ke Karamar Hukumar Safana.

 

Yana daga cikin wadanda suka taba amsar tuba, har yana halartar duk tarurrukan sasanci da aka rika yi. Ya taba ajiye makami, har ma ya ba da wasu bindigu.

 

Daga baya ya koma ruwa, ya yi juyin mulki, inda ya kashe wasu shugabannin daba biyu ya yi gadon yaransu da yankin da suke iko da su.

 

Kafin a kashe shi, bayanai sun tabbatar ya fara magana da kungiyoyin Boko Haram masu neman wajen zama a dajin Rugu. Dajin da ya hada Kananan Hukumomi biyar na Katsina, ya kuma hada jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna da kasar Nijar.

 

Majiyarmu ta ce an dade ana shirin kisan nasa. Sojan sama sune suka yi aikin dauko taswirar inda yake.

 

Jami’an tsaron farin kaya na kasa sune suka tabbatar da yana cikin gidan.

 

Ba da jirgin sama aka kashe shi ba kamar yadda ake tsammani.

Mizayil ne, aka harba ta kasa, wanda ya tafi a kan yadda aka tsara shi da saita shi, kuma aka yi nasara inda aka hara.

 

Masana harkokin tsaro sun yi imani cewa, a yakin da ake yi da barayin daji, rashin hadin kai da aiki tare tsakanin jami’an tsaro da ke fadan yana daga cikin abin da ke kawo koma baya da kafar Ungulu.

 

Bincikenmu ya gano idan aka samu cikakken hadin kai tsakanin jami’an tsaron da ake da su, labarin zai iya canzawa.

 

Katsina City News

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar Taskar Labarai

@ www.jaridartaskarlabarai.com

The Links News

@ www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

Email.katsinacitynews2@gmail.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here