“Bayan jami’an tsaro: “Ba zamu samu Aminci ba ace wasu su zo su bamu tsaro” -Mai Unguwar Shola Quarters a Katsina

0

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

 

Biyo bayan harin masu garkuwa da mutane a Unguwar Shola Quarters dake yammacin Katsina bayan asibitin koyarwa ta Gwamnatin Tarayya a garin na Katsina a  ranar Asabar da ta gabata.

 

Mazauna Unguwar sun shiga fargaba inda suke bacci da ido ɗaya kamar yanda wasu mazauna Unguwar suka shedamana. Wannan harin shine na biyu kuma wanda aka samu Asarar rayuka a cikinsa, kimanin watanni biyu da suka gabata an taba kai harin makamancinsa inda aka tafi da wani mazaunin Unguwar sai da aka biya kudin fansa kana aka sako shi. Sai gashi kuma a ranar Asabar ta 7 ga watan Agusta maharan sun shiga Unguwar inda suka kashe mutum biyu da yin garkuwa da Amarya da ango wanda ya zuwa hada wannan rahoton maharan basu sako su ba.

 

Cikin zaman ɗarɗar da rashin tabbas jiya da rana tsaka Unguwar ta Shola Quarters ta shiga wani ruɗani inda akayi ta guje-guje ba babba ba yaro matan Aure da tsofi.

 

Da Katsina City News ta je domin jin abinda ya faru ta gano cewa wasu mahara ne daga nisan kauyen da ke can kurya ana ce da kauyen Nasarawar Bugaje, barayin sun gitta zasu wuce inda kuma jami’an tsaro suka yunƙura da nufin daƙile su don kada su shiga cikin garin na Katsina, inda akaji ƙarar harbe-harbe wanda hakan ya haddasa mazauna Unguwar shiga ruɗani da tunanin ko wajen su aka yo.

 

Da safiyar yau Laraba wasu matasa mazauna Unguwar ta Shola, suka shirya wani gangamin da kwalaye riƙe, suna ɗagawa suna cewa “Suna buƙatar tsaro, idan babu tsaro ba zaɓe.” Suna kira da Gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa akan rayukan su.

See also  Jami'an Tsaro sun kama wani dalibi Saboda yaci zarafin Matar shugaban kasa.

 

Da muke zanta da mai Unguwar yankin na Shola Quarters ya yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro kwarai da gaske inda ya tabbatar ma Jaridun mu na Katsina City News cewa “Tabbas jami’an tsaro suna iya kokarin su akan kare unguwar mu, duk lokacin da wani abu ya faru ko mukaga alama zai faru muna kiransu kuma suna yin abinda ya dace, saidai kawai wani al’amari da zamuce saidai addu’a saboda suma kansu jami’an tsaron basu tsira ba. Muma mazauna unguwar muna taimakawa ƴansanda sabida muna da kwamitin Unguwa dake sintiri, a cikin su ne ma aka kashe wasu lokacin da wannan harin ya afku.” Inji shi.

 

Sana yace duk wani jami’in tsaro na Gwamnati ko wanda Gwamnati ta yarda da shi muna goyon bayan sutaimaka mana da tsaro, amma bamu yarda wasu masu kaki da suke don raɗin kansu ba ace su zo cikin Unguwar mu wai don bata kariya, yace wadannan ba zamu aminta da suba. Ya kara da cewa, an taɓa kawo wasu da suka maida wajen sansanin ‘Yan shaye-shaye, saboda kawai wai suna sanya kaki.

 

A karshe yayi kira ga mazauna Unguwar da su kwantar da hankulan su, kuma su daina yaɗa jita-jita abinda ya faru a jiya wanda ya sanya matan Aure hawan katangu da gujewa gidajensu duk jita-jita ce ta jawo shi. Inji Mai Unguwar Shola Quarters.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here