Daga Zahraddeen Sirajo Abbas
Gangamin da suka fara gudanarwa da sanyin safiyar yau Litinin a Unguwar ta Shola Quarters dake bayan Medical Center cikin Garin Katsina, masu gangamin sun fito da kwalen da suka rubuta cewa babu tsaro ba zabe, Gangamin ya shafi Maza Yara da manya da mace daya.
Abunda ke nufi kamar yadda wani da yaso a sakaya sunanshi ya shedawa wakilinmu cewa “lallai ba zasu yi zabe mai zuwa ba matukar ba’a samu tsaro a cikin Unguwar ba, dama Jahar ta katsina baki daya, ya cigaba da cewa jiya a cikin Unguwar ko motsin Tsuntu babu balle a samu wani Gidan da ke a Mutane”
Haka wani daga cikin Mutanen Unguwar ya dake sheda mani cewa “daga kashi 90 cikin 100 na Mutanen Unguwar duk suna gudun hijira a wasu unguwannin, saboda haka ya kamata Gwamnati ta sani muna cikin mawuyacin hali na firgici da tashin hankali, dan Allah su taimaka mana mu samu tsaro da zaman lafiya.
A nashin bangaren Mustapha musa cewa ya yi “ina kira ga al’umma dasu kwantar da hankalinsu wajen sanin hakikanin abunda ke faru, kada daga an ce kaza a kama guje guje hakan na iya yiwuwa jita jita ce ko karya, saboda akan samu irin wannan matsalar wasu su dunga tadawa wasu hankali.
Ya kamata ace kuna bada shawarar yadda mutane zasu dauki makamai su dinga tsare kansu. Ba labaran ban tsoro ba kullum