YAKIN NEMAN ZABE: NNPP TA ROKI INEC DA TA HUKUNTA DIKKO RADDA

0

Muhammad Kabir

@ Jaridar Taskar Labarai

Jam’iyyar New Nigerian People’s Party, NNPP, reshen jihar Katsina, ta shigar da kara a gaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, kan dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Alhaji Dikko Radda, kan ya yi yakin neman zabe kafin ranar da INEC ta sanya.

INEC ta sanya ranar 12 ga Oktoba domin fara yakin neman zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha da kuma ranar 28 ga watan Satumba domin fara yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.

Sanarwar wacce ke dauke da sa hannun shugaban NNPP na jihar Alhaji Sani Liti, ta ambato sashe na 28 na dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima wanda ya yi karin bayani kan abubuwan da suka dace na dokar.

“Mun rubuta ne domin sanar da ku yadda aka karya dokar zabe, muna roko da a hukunta wadanda suka karya doka kamar yadda doka ta tanada.

“Mun lura da yadda dan takarar jam’iyyar APC, Umar Dikko Radda, ya fara yakin neman zabensa a kananan hukumomin Baure, Zango da Sandamu ba tare da mutunta dokar ba,” in ji sanarwar.

Shugaban na NNPP ya bukaci INEC da ta kama tare da gurfanar da wadanda suka karya dokar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dikko Umar Radda tare da sa su fuskanci fushin doka.

Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai
@www.taskarlabarai.com

The links news
@ www.thelinksnews.com

07043777779 .08137777245

Email: katsinacitynews2@gmail.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here