Sharhin Jaridun Katsina City News
Yanzu dai ta tabbata ‘yan ta’addar da ke da sansani a Katsina suna da mummunar manufar tsorata mutanen karkara da mai da su masu yi masu biyayya. Sai kuma auka wa babban birnin na Katsina.
Kauyukan dake Gaf da katsina suna ta mika masu wuya,kar su cutar dasu su kuma ba ruwansu dasu.
Ta tabbata jami’an tsaron da ake da su ba za su iya ba da kariyar da jama’a ke tsammani ba.
In za ayi ma jami an tsaron adalci, aikin yayi yawa ba karfin gwaiwa ba isassun kayan aiki.
Babban jami in tsaro a jahar, shine gwamna,ya bayyana ma duniya gaskiya.itace,kowa ya kare kanshi.
Misalai da yawa sun tabbatar da haka wadanda aka gani kuma aka san su.
Za mu ba da misali kwara daya tilo, wanda ya faru a ranar Talata 9 ga watan Agusta.
Ya ta’adda da mashin takwas su 16 da bindiga 10 da karfe 1 na rana suka tare hanyar Jibia zuwa katsina ko katsina zuwa jibia.
A gefen inda suka tare, hadin gwiwar jami’an tsaro ne, soja, ‘yan sanda, kwastam da kuma imigireshen, da motocin APC guda biyu.
Haka aka rika kallon-kallo tsakaninsu da jami’an tsaron, kamar yadda daya daga cikinsu ya tabbatar wa jaridunmu.
Motocin da suka tsaya a tsakanin gefen Jibia da Katsina sun fi 300. ‘Yan ta’adda 16 suka kawo wannan tsaikon.
Jami’an tsaro sama da 40 a gefe daya suka kasa fada masu.
Ganau ya ce, ‘yan ta’addar sun rika yi wa jami’an tsaronmu gwalo da dakuwa da kiran in sun isa su taho a gamu.
‘Yan ta’addar nan su 16 haka suka rike wannan babbar hanyar da rana kata tsawon awanni biyu. Sannan suka hau baburansu suka koma daji.
Muna da wasu misalan da suka faru, amma wannan dayan ya isa isar da sako.
Mu a Katsina City News muna kira ga al’ummar Katsina su dau darasi irin na Maiduguri, lokacin da suka ga ‘yan Boko Haram suna son tsorata da mamaye babban birnin suka fito da hanyoyin kare kansu.
Wannan ya jawo sai da birnin Maiduguri ya fi na Abuja tsaro kamar yadda rahoton tsaron birane na shekarar 2016 ya nuna.
Sun samu tsaron ne, ba ta jami’an tsaro ba, amma ta aikin kare kai wadanda suka shimfida a tsakaninsu.
Mu a Katsina City News muna ganin in har muka dogara ga jami’an tsaro zalla, to tabbas za a yi ta kisan mutane kamar kiyashi, a yi ta kama su kamar ‘yan tsaki.
Ya kamata Attajiranmu su hada wata gidauniya ta samar da kudi da za ta samar da masu tsaro irin na Maiduguri bisa tsari da kuma doka.
Ya kamata mutanen Katsina su fahimci hatsarin da ke gabanmu. Yaki ne har daka zai ci mu, dole ne kowa ya san ya zai kare kansa. Dole ne mu zame sojoji zallarmu.
Iyayenmu kuma shugabanninmu, Malamai na gaskiya suna yin nasu wajen addu’a ba dare ba rana.
Dukkanin masallatai da wurin ayyukan ibada ba sa wasa da addu’o’i na tsari da kariya ga al’ummarmu baki daya.
Wadannan addu’o’in da Malamai ke yi mana sune babbar garkuwa da sulke da kansakali a wajenmu.
Abin da ya rage MU TASHI MU KARE KANMU, KO MU ZAMA BAYI A GIDAJENMU.
Wannan shine Matsayin jaridun katsina city news,the links news da jaridar taskar labarai.