Mu’azu Hassan
@ Katsina City News
Dan takarar Gwamna a jam’iyyar APC, Alhaji Dikko Umar Radda, ya kafa wani kwamiti mai membobi biyar domin gano masa matsalar jam’iyyar APC a Jihar Katsina.
Membobin sune; Hon. Musa Nuhu Gafiya, dan majalisar da ke wakiltar Kaita; Hon. Gide Sabuwar Kasa daga yankin Funtua; Hon. Yahaya Galadima daga yankin Katsina; Alhaji Sule Aruwan Ingawa daga yankin Daura; sai Malam Yakubu Suleiman a matsayin Sakatare.
Dan takarar ya ba kwamitin aikin ya kewaya duk fadin Jihar Katsina domin ya gano matsalolin jam’iyyar APC da kuma yiyuwar cin nasara a zabe ko akasin haka.
Kwamitin ya kammala aikin nasa, har ya mika rahoton ga dan takarar a karshen makon da ya gabata.
Wasu da aka tattauna da su sun fada wa jaridunmu cewa, kwamitin ya tsara ganawa da wasu ‘yan jam’iyya ne a kowace Karamar Hukuma.
Sun ce an gana da mata, matasa, matsaikaita, da dattawa.
Kusan kowace Karamar Hukuma tana da irin tata matsalar, kamar yadda wani dan yankin Funtua da aka yi magana da shi ya tabbatar mana.
Rahoton da aka tattara yana da shafuka masu yawa, sannan yana dauke da sunayen duk wadanda aka yi magana da su.
Matsalolin da aka gano wadanda suka shafi jam’iyyar APC a rahoton sune:-
1). Kusan dukkanin Kananan Hukumomin Katsina suna fama da matsalar tsaro, in ban da guda tara kacal. Wannan kuma na iya shafar nasarar jam’iyyar.
2). Siyasar gida-gida. Kusan kowace Karamar Hukuma da yanki akwai masu gida da suke da karfi, kuma su ke juya siyasar Karamar Hukumar ko yankin.
3). Rashin cika alkawarin baya. A wasu Kananan Hukumomi an yi masu alkawarin a baya kuma ba a cika ba, suna rike da wannan.
4). Rashin hasafi. A rahoton ‘yan jam’iyya sun yi korafin ba kula da su ba, wajen ba su taimakon da ya dace a lokacin bukata. Wasu ‘yan kalilan sune suka rika ci da gumin sauran.
5). Rahoton ya zargi wasu ‘yan Majalisun Tarayya da yin biris da wasu Kananan Hukumomin da aka zabe shi tare da su. Misali mutanen Dutsi, sun zargi Mansir Ali Mashi da cewa ba ya yi da su. Haka mutanen Ingawa sun zargi Yahaya Kusada ba ya yi da su. Haka nan a rahoton an zargi Hamza Sule Faskari da yadda ya so a siyasar Faskari da Sabuwa.
6) Rahoton ya bayyana wasu da suka ji hushi suka koma gefe daya, duk da kuwa wadansu da su aka faro tafiyar. An ba da shawarar a bi su a dawo da su.
Rahoton ya ba da shawarwarin yadda za a gana da mutane domin neman goyon bayansu.
Wannan aikin da dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC ya yi, ya yi kama da wanda wata kungiya, tare da hadin gwiwar Kamfanin Matasa Media Links masu buga jaridun Katsina City News suka yi mai taken; Ko Jam’iyyar APC Za Ta Iya Kafa Gwamnati A Katsina A 2023?
Aikin hadin gwiwar an kammala shi, har ma kungiyar da ta dau nauyin yin sa ta tafi da rahotonta.
Abin da aka gano hakkin kungiyar da ta dau nauyin aikin ne ta fitar da shi lokacin da ya yi mata.
Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245