Zaharadeen Ishaq Abubakar @Katsina City News ?️
Garin gora dake da tazarar kusan Mil goma sha biyar daga ƙaramar Hukumar Safana suna fuskantar hare-haren’yan bindiga, inda suka sheda ma Katsina City News cewa a ƙasa ga wata guda ankai masu hari sau tara.
A hare-haren baya-bayannan shine wanda ya faru sau huɗu harin farko da na biyu sun kwashi dabbobi inda na uku da na huɗu suka kwashi mutane. Majiyar ta tabbatar mana da sun dauki wata uwa da ɗiyarta inda daga bisani suka sako su. A jiya juma’a wayewar garin Asabar sun kwashe wasu ɗalibai mata guda biyu da suka samu hutun Makaranta suka dawo gida da matar Aure guda, inda ya zuwa haɗa wannan rahoto suna hannun masu garkuwa da mutanen a inda suka harbi wani matashi a kafa kokarin kare kai, majiyar mu ta tabbatar da yana Asibitin koyarwa ta Katsina.
Mazauna garin na Gora sun koka akan zargin rashin kulawar jami’an tsaro, sunce ɓarayin suna shiga garin Gora suyi ta harbe-harbe amma babu wani gudumawar gaggawa daga garesu duk da kuma suna da sansanin su a wajen gari wajen makarantar da za’a iyacewa ta haɗe ma da garin.
Al’amarin rashin tsaro yayi ƙamari a jihohin Katsina, Kaduna, Zamfara inda ko a kwana-kwanannan Gwamnonin jihohin Katsina da Zamfara sunyi kira ga al’umma su dauki matakin kare kansu. A wani Faifan Bidiyo da yake yawo a Kafafen sada zumunta, anga Gwamnan Katsina Aminu Masari yana kausasa magana ga jami’an tsaro cewa “Mun sani cewa ku Mutane ne kamar mu, amma tunda kuka zaɓi zakuyi Aiki irin wannan babu dalilin da za’a kiraku kuki zuwa, ko kuma wani ya ɗauko labarin ya baku, amma kuje ku saida ransa a wajen wani cewa ai wane ya gaya mani.” Yace kuji tsoron Allah bayan nan akwai makoma inda za’a haɗu da mahalicci. Don haka abinda kai shi zakagani.” Gwamnan ya ƙara da cewa duk wanda ya ƙi labarin ƙarya da labarin banza to na kirkin ma da wuya ya samu.
Ya zuwa haɗa wannan rahoton mun samu labarin masu garkuwa da mutane sun tare fasinjoji da suka fito daga garin Batsari zuwa wajen biki a wata Mota ƙirar Sharon, dukkanin su ankorasu Daji sai wata tsohuwa da ta tsira daga cikin su.