Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje halarci taron karrama yan asalin Jihar Kano dasuka samu manyan mukamai a Gwamnatin Tarayya dakuma wanda suka hidimtawa Jihar Kano

0

A daren jiya ne Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR da Mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna sun halarci taron karrama yan asalin Jihar Kano dasuka samu manyan mukamai a Gwamnatin Tarayya dakuma wanda suka hidimtawa Jihar Kano a fannin aiki wanda Gidauniyar masu kishin Jihar Kano suka shirya a dakin taro na Amani dake kusa da Titin Audu Bako a Jihar Kano.

 

Cikin wanda aka karrama akwai Sabon Ministan ayyuka da gidaje na Jiha wato Hon. Umar Ibrahim Elyakub, Babban Mai Taimakawa Shugaban Kasa akan Harkokin Majalisa Hon. Nasiru Babbale Ila, Kwamishinan yan Sanda mai tafiya CP Samaila Dikko da Sauransu.

 

Daga bisani a wajen taron an karrama Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR da Hon. Alhassan Ado Doguwa bisa Gudummawar da suka bawa harkokin Tsaro a Jihar Kano.

 

Taron yasamu halartar Masu Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero dana Hadeji Alh. Adamu Abubakar Maje, Sanatoci, Yan Majalisun Tarayya, Shugaban Jamiyyar APC na Jihar Kano Alh. Abdullahi Abbas, manyan Malaman addini, yan kasuwa, jami’an tsaro da yan Siyasa.

 

Abubakar Aminu Ibrahim

SSA Social Media,Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here