Gwamnatin Jigawa Ta Rufe Makarantu Saboda Rashin Tsaro

0

Kwana biyu kenan da rufe makarantun gaba da sakandare, gwamnatin jihar Jigawa ta bayar da umarnin rufe makarantun gwamnati cikin gaggawa sakamakon barazanar tsaro.

 

Gwamnan jihar Muhammad Badaru Abubakar ya bada umarnin ne bayan samun cikakken rahoto kan yiwuwar kai hari a makarantun da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka shirya.

 

Sakamakon haka rufe makarantar ya katse sanyawa da rubuta jarabawar talla da daliban ke yi.

 

Da aka tuntubi kwamishinan ‘yan sandan, Mista Sale Tafida ta bakin mai magana da yawun rundunar, DSP Lawal Shisu ya ce, “Ba mu ba da shawarar rufe makarantu ba. A gaskiya babu wanda ya tuntube mu dangane da haka.”

 

Kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha na jihar, Mista Lawan Yunusa Danzomo ya tabbatar da cewa an rufe makarantun ne saboda kalubalen tsaro.

 

Ya ce, “Eh mana, mun rufe makarantu ne bisa rahotannin sirri na barazanar tsaro kuma muna aiki tare da duk masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali da muke samu a jihar.

 

“Mun kuma umarci jami’ar da ta kara sanya ido kan tsaro tare da hada kai da al’umma da sauran masu ruwa da tsaki domin tattara bayanai da kuma daukar matakin da ya dace kan duk wani hari ko zagon kasa ga jami’an tsaron jihar.”

 

Da yake mayar da martani game da rufe makarantun, wani Malam Imurana Malami Ibrahim wanda shi ne shugaban kungiyar malamai ta iyaye (PTA) a daya daga cikin makarantun ya nuna rashin jin dadinsa da matakin da gwamnatin jihar ta dauka, inda ya zargi gwamnati da jefa ‘ya’yansu da unguwanni cikin hadari.

 

Ya ce, “Na ji takaici a gwamnati, ta yaya za ku yi ba zato ba tsammani kuma a cikin sa’o’i kadan za ku ba da umarnin rufe makarantun tare da fitar da yaran ba tare da wani kyakkyawan tsari na yadda yaran za su isa gida lafiya ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here