Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alh Mannir Yakubu FNIQS ya halarci taron Kungiyar Gwamnonin Najeriya da aka gudanar a ranar larabar da ta gabata a babban dakin taro na fadar Gwamnatin tarayya da ke Babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Taron ya yanke shawarar karin kasafin kudaden da ake warewa don inganta kula da lafiya tun daga matakin farko don samun nasarar shirin na wannan shekarar.
Gwamnan Jihar Ekiti wanda kuma shine Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya Kayode Fayemi shine ya jagoranci zaman da ya samu halartar Gwamnoni daga jahohi 35 na Najeriya.
Majalissar tayi alwashin kara daukar ma’aikatan lafiya a Jahohi domin tabbatar da cewa an samar da ma’aikatan lafiyar da asibitoci ke bukata.
Haka zalika, Fayemi ya baiyana cewa Gwamnonin jahohin 36 sun yi alkawalin fitar da dukkanin kudaden da aka amince dasu cikin kasafin kudi domin kula da lafiya tun daga matakin farko.
A lokacin da yake taya Gwamnonin jahohin 36 na Najeriya murnar amincewa da shirin hadin guiwa na kula da lafiya a matakin farko, Daraktan Gidauniyar Bill and Melinda Gates ya baiyana cewa, shirin zai bada damar cimma kudurorin Gwamnonin a bangaren kula da lafiya.
A jawabinsa mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad III ya jaddada bukatar da ke akwai na karin kudaden kula da lafiya a cikin kasafin kudi.
A bangaren Gwamnatin Jihar Katsina, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina QS Mannir Yakubu daya wakilci Gwamna Masari ya samu rakiyar Kwamishinan lafiya na Jihar Engr. Yakubu Nuhu Danja.