‘Yan sanda a jahar katsina sun dakile Kai Wani hari sannan suka ceto mutane 2 da aka yi garkuwa da su

0

‘Yan sanda a jahar Katsina sun ce sun kashe ‘yan ta’adda da dama tare da raunata wasu da dama a lokacin da suka dakile wani hari a kauyen Wapa da ke karamar hukumar Kurfi a jihar tare da ceto wasu mutane biyu da aka sace.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Sufeto Gambo Isah a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce, “Yau 19 ga watan Agusta da misalin karfe 1:00 na dare, ‘yan ta’adda su 24 a kan babura, suna harbi lokaci-lokaci da bindigogi kirar AK 47, sun kai hari kauyen Wapa da ke karamar hukumar Kurfi. na jihar Katsina tare da yin garkuwa da wasu mutane su biyu Alhaji Aminu Wapa da Wada Sale na kauyen Wapa, a karamar hukumar Kurfi”.

A cewar Isah, bayan samun labarin, rundunar ta tura jami’anta zuwa yankin inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan.

Ya ce, rundunar ta samu nasarar fatattakar ‘yan ta’addan tare da kubutar da duk wadanda aka yi garkuwa da su, an kashe ‘yan ta’adda da dama tare da raunata su a yayin arangamar.

ya kara da cewa, har yanzu tawagar ‘yan sanda na ci gaba da yin sintiri a yankin da nufin kamo ‘yan ta’addan da suka raunata tare da gawarwakinsu.

Tuni dai kwamishinan ‘yan sanda, Idrisu Dabban ya yaba da kokarin da jami’an suka yi na dakile ‘yan ta’addan.

Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here