Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya musanta goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu a kan takwarorinsa na Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, da Peter Obi na jam’iyyar Labour.
Idan za a iya tunawa, Tinubu a ranar 17 ga watan Agusta, 2022, ya ziyarci tsohon shugaban kasar a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun.
Wadanda suka raka Tinubu sun hada da tsoffin gwamnonin jihar biyu, Olusegun Osoba da Gbenga Daniel; tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa, Bisi Akande; Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila; tsohun Shugaban Hukumar EFCC Nuhu Ribadu da dai sauransu.
Gbajabiamila ya shaida wa manema labarai a Legas cewa Obasanjo ya yi kalamai masu karfafa gwiwa game da burin Tinubu har ma ya yi addu’a ga dan takarar shugaban kasa na APC.
Ya kara da cewa Obasanjo ya baiwa Tinubu tabbacin samun nasara a zaben.
Sai dai kuma da yake mayar da martani kan ikirarin, Obasanjo ya ce maganar da ake yi masa karya ce, kuma mutanen da ke da wannan rahoto ba su taimaka wa dan takarar ba.
Tsohon shugaban kasar a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi, ya fitar a ranar Asabar, 20 ga watan Agusta, 2022, ya bayyana wasu magoya bayan Tinubu a matsayin makiya.