Yan Sanda A Jihar Katsina Sunyi Nasarar Kashe Wani dan ta’adda da kwace muggan makamai a hannunsu da Kama Wasu da ake Zargi da Bada bayanan sirri ga Yan bindigar.

0

YanKakakin rundunar ‘yan sanda SP Gambo Isah a cikin wata sanarwa da ya fitar, yace A ranar 20/08/2022 da misalin karfe 07:30 na dare, sunsamu wani bayanan sirri cewa an ga ‘yan ta’adda a wani kauye Maizuma da ke karamar hukumar Danja ta jihar Katsina, DPO na yankin karamar Hukumar Danja ya jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa yankin

 

Rundunar ta samu nasarar fatattakar ‘yan ta’addan tare da kashe daya daga ciki, Sunkuma Samu Nasarar kwace bindiga kirar gida da kakin sojoji da adduna da kwalabe da Babura Biyu da sauran Wasu kayan anfani.

 

An kuma kama wani da ake zargin mai ba wa ‘yan ta’adda bayanai ne.

See also  An Yi Jana'izar Mutanen Da Suka Mutu A Hatsarin Kwale-Kwale A Neja

 

Kwamishinan ’Yan sandan na Jihar Katsina, CP Idrisu Dabban Dauda ya yaba da kokarin da jami’an suke wajen dakile ‘yan ta’addan, ya kuma umarce su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu har zuwa lokacin da za a magance duk wani nau’in laifuka.

 

Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai a yakin da ake yi da ta’addanci a jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here