An kai sabbin kwamishinonin ƴan sanda zuwa Kano, Zamfara da Enugu

0

Hedkwatar Rundunar Ƴan Sanda da ke Abuja ta tura sabbin kwamishinonin ƴan sanda zuwa jihohin Kano, Zamfara da Enugu.

 

Kamar yadda sanarwar ‘yan sanda mai lamba TH.5361/FS/FHO/ABJ/SUB.4/715 ta nuna, an tura Abubakar Lawal zuwa jihar Kano, yayin da Yusuf Kolo aka tura jihar Zamfara.

 

Sanarwar ta ce ta ci gaba da cewa an kuma tura Ahmed Ammani zuwa Enugu.

 

Sanarwar ta ƙara da cewa aikin nasu ya fara nan take.

 

Sabon kwamishinan na Kano CP, wanda aka yi masa canjin wajen aiki daga jihar Enugu, ya taɓa zama baturen ƴan sanda (DPO) na Caji-ofis ɗin Hotoro a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here