TARIHIN MARIGAYI KAURAN KATSINA ALH. NUHU ABDULKADIR.

0

An haifi Kauran Katsina Alhaji Nuhu Abdulkadir a cikin garin Rimi a 1945 a gidan da yake Sarauta a halin yanzu.

Kaura Abdulkadir ne, tsatson Kaura Muhammadu na Banye mahaifin Kaura Abubakar wanda ya sari garin Rimi. ya fito daga daular Fulani.

A lokacin kuriciyarsa ya yi Karatun addinin Islama a wajen Mallam Aminu wanda ke zuwa a gidansu ya koyar da su karatun Al Kur’ani mai Girma da sauran hukunce hukuncen shari’ar Musulunci. Ya shiga Makarantar Elementary da ke Rimi a 1954 zuwa 1957, ya wuce siniya firamare da ke Rafindadi daga 1958 zuwa 1960. daga nan ya wuce makarantar sakandare ta Provicial dake Katsina wadda a halin yanzu ake kira (Government College Katsina) ya kammala karatun sakandare a 1966.

A shekara ta 1981 Allah ya yi wa dan’uwansa Kado Dikko rasuwa, don haka ne sai ya nemi sarautar mahailinsa. Kuma Allah ya tabbatar masa da ita.

Sarkin Katsina Allhaji Dr. Muhammadu Kabir Usman ya nada shi a ranar 24/12/1982 don ya gaji sarautar mahaifinsa, shine Kaura na goma sha ukk (13) da ke sarautar Kauran Katsina CIkin iyalan Muhammadu Na banye Yana da matan aure hudu da ya’ya ashirin da daya (21)

MATAN AURE:

1. Hajiya Amina (Asabe)

2. Hajiya Salamatu

See also  Bidiyon Sirri; Yadda Akai Binciken gidajen badala da masha'a a birnin katsina.

3. Hajiya Binta

4. Hajiya Wasila

 

YAYA

1. Aisha

2. Late Wakili Usman

3. Alhaji Aminu Ciroma

4. Lubabatu

5. Amina (Kilishi)

6. Farida

7. Abba (Tanimu)

8. Suleiman

9. Ramatu

10. Abdulkadir (B.B)

11. Mubarak

12. Rabi

13. Badamasi

14. Zulai

15. Fatima

16. Hamza

17. Nuhu

18. (Khalifa) Lawal

19. Hafsat

20. Dikko

21. Usman

 

MUTANEN DA SUKA YI SARAUTAR KAURAN KATSINA.

 

1.Kaura Muhammadu Na Banye 1800-1811

2. Kaura Abubakar (Dan Na Banye)1814-1854

3. Kaura Usman (Dan Na Banye) 1854-1856

4. Kaura Isiyaku (Dan Na Banye) 1856-1889

5. Kaura Halu (Dan Abubakar) 1889-1895

6. Kaura Wayya (Dan Isiyaku) 1895-1897

7. Kaura Yusut Dan Usman 1897-1907

8. Kaura lanimu (Dan Abubakar) 1907-1933

9. Kaura Abdulkadir (Dan Tanimu)1933-1967

10 Kaura Mamman (Dan Abdulkadir)1967-1974

11. Kaura Dikko (Dan lanimu) 1974-1978

12. Kaura Abdulkadir ll (Dan Dikko)1978-1981

13. Kaura Nuhu (Dan Abdukadirl) 1982- 2022

 

Kauran Katsina Alhaji Nunu Abdulkadir mutum ne mai son jama’a, bin hakkin talakawa, mai kaifin hankali da hangen ya kamata, yana da hakuri da daukar shawara.

Yana sha’awar karatun Al Kurani Mai Girma, wasa da doki, kiwo da Noma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here