Muazu hassan
@ katsina city news
Yan bindiga sun tare hanyar Jibia zuwa katsina yau laraba da misalin karfe hudu da Rabi na yamma.
Wani da ya tsira da kyar, ya fada ma jaridun katsina city news cewa yan bindigar sun tare hanyar kusa da wani kauye mai suna Kadobe.
Ganau, yace yan bindigar bisa Mashin Tara goyon daya suna da bindigu kwara bakwai.
Ganau, yace yan bindigar sun harbi wasu motoci biyu na ukun ya tsaya.yace sun harbi mutane biyu a motocin, sun kuma debi mutane a mashi na suka shiga dasu daji.
Ganau yace yan bindigar sun dau tsawon mintun biyar a hanyar kafin su gama ta ‘asarsu su, koma daji.
Ganau,yace ya tsira ne daga mota ta uku da aka tsayar inda ya yanki daji da ya lura hankalin yan bindigar na ga motoci biyun farko.
Munyi kokarin jin ta bakin Rundunar yan sanda amma bamu samu ba.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Email. Katsinacitynews2@gmail.com