Hukumar EFCC shiyyar Kano ta kama wani mai suna Gazali Ado , mai shekaru 35 da ya yi sojin gona a matsayin jami’in hukumar EFCC a sashen Google map.

An kama shi ne bayan wani korafi da wani mai suna Kenneth Nwarize ya rubuta inda yake zaargin shi da zambatar shi kudi N150,000 (Naira Dubu Dari da hamsin).
Wanda ya kawo korafi ya yi zargi cewa ya samu lambar waya (+2348115177852) ta wanda aka kama lokacin da yake binciken sashen hukumar ta yanar gizo inda yake so ya kawo korafi, ya kira lambar sannan wanda ake zargi ya bukaci ya bashi kudin.
Ya bayyana cewa ya tura kudin cikin asusun banki na wani Ibrahim Mohammed.
An kama Gazali tare da Sanusi Abubakar Liman da Ibrahim Mohammed.
Za’a gurfanar da su gaban kotu bayan an kammala bincike.
Hukumar EFCC na kira ga alúmma da suke tunanin an zambace su da su kawo korafin su akan wannan number.
Source: EFCC FB Page