GWAMNATIN JIHAR KATSINA TA GARGADI MATASA AKAN SHIGA BANGAR SIYASA

0

Gwamnatin Jihar Katsina ta ja hankalin matasa da kada su yarda baragurbin ‘yansiyasa su yi amfani da da su wajen tayar da hargitsi a lokuttan zabubbukan dake tafe.

 

Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Malam Muntari Lawal ya yi wannan gargadin a yayin da Majalissar Matasa ta Nijeriya reshen Jihar Katsina ta kai ma shi ziyara a ofishinsa.

 

Malam Muntari Lawal ya ankarar da matasan akan wasu marasa kishin kasar nan da ka iya tunzura su a tada hargitsi a yayin zaben don cin ma wata manufa tasu ta wargaza hadin kan kasar nan.

 

Sakataren Gwamnatin ya ce idan suka sake hakan ta afku, to galibi matasan ne za su cutu saboda sune ke da sauran shekaru da yawa nan gaba.

 

Don haka ya ce a matsayin kungiyar su wacce ba ta siyasa ba kuma ta dade da kafuwa a kasar nan wajibi ne shugabanninta su tashi tsaye don kange matasa daga fadawa hannun marasa kishin kasa.

 

Ya yi alwashin cewa a nata bangare, Gwamnatin Jihar Katsina za ta ci gaba da tallaba masu ta hanyar aiwatar da ayyukan raya kasa da na bunkasa rayuwar mata da matasa bakin karfinta.

See also  FG TO PRIORITIZE COMPLETION OF KANO-KADUNA RAIL PROJECT – TRANSPORTATION MINISTER. 

 

Malam Muntari Lawal ya sheda wa Majalissar cewa a ko da yaushe a shirye yake da ya saurare su idan bukatar hakan ta taso.

 

Tun farko a jawabinsa shugaban Majalissar Matasan, Kwamared Shamsuddini Ibrahim Shamo ya ce sun kawo ziyarar ce don jinjina ma Gwamna Aminu Bello Masari akan aiyukan raya kasa da Gwamnatinsa ke gudanarwa duk kuwa da yanayin matsin tallalin arziki da barazanar tsaro da ta addabi jiha da kasa baki daya.

 

Wata sanarwa wadda Daraktan Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Abdullahi Aliyu Yar’adua ya raba ga manema labarai, ta ce shugabannin Majalissar Matasan sun yi alwashin ci gaba da yin gangamin fadakar da ‘yanuwansu matasa akan illolin tu’amalli da miyagun kwayoyi da aikata miyagun laifuka kamar su harkar kauraye da ta’addanci da kuma bangar siyasa.

 

Daga karshe Majalissar Matasan ta mika Lambar Yabo ga Malam Muntari Lawal a matsayinsa na uba wanda yake tsaye wajen tabattar da bunkasa rayuwar matasan jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here