Hon. Danlami Muhammad Kurfi, da ya samu mukamin Board Chairman Rural Electrification Agency (REA) wato Shugaban Hukumar kula da samar da wutar lantarki a Karkara ta Najeriya. Wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya bashi a satin da ya gabata.
Danlami yayi godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari akan damar da ya bashi, yace “Insha Allahu zanyi amfani da wannan damar a karkashin Ofishina inga na samarwa yankunan Karkara, duk wani abu da yake dama hakkin Ofishinana ne,” yace ko babu komai dama ni daga karkara na fito kuma nasan matsalolinta, Kurfi ya bayyana irin yanda aka bar yankunan karkara a baya wajen ababen More rayuwa, yace shiyasa ma ake samun masu garkuwa da mutane a cikinsu.
Hon. Kurfi yayi wannan bayanin ne a lokacin da ya gayyaci Shuwagabannin jam’iyyar APC na mazabarsa ta Barkiya Ward, a Karamar hukumar Kurfi, domin tattauna wasu al’amura da suka shafi APC na cikin gida, Injishi.
Danlami ya jajanta game da matsalar tsaro da yace a satin da ya gabata ya samu labarin masu garkuwa da mutane sun shiga garin na Barkiya da wasu Unguwanni makwafa, inda yace, abinda ke gabanmu a halin yanzu shine addu’a, saboda ba magana bace ta wata jam’iyya a’a al’amari ne da ke bukatar sa ido da addu’a.
A karshe Danlami kurfi ya kara tabbatar ma ‘Yan uwansa na mazabar Barkiya a ƙarƙashin jagorancin shuwagabannin Jam’iyyar APC na Barkiya Ward cewa duk wani tallafi ko wane irine da zai samar da tsaro a yankin a shirye yake dama yanayi, kuma zai kara.
Chairman na APC Barkiya Ward yayi godiya da irin gudummawar da Hon. Danlami Kurfi yake basu a matsayinsu na ‘Ya’yan jam’iyyar APC, kuma yasha Alwashin jajircewa domin samar da kyakkyawan hadin kai a tsakanin’ya’yan jam’iyyar.
Daga karshe tsohon Kansilan riko na Barkiya Ward yayi karin haske akan ire-iren ayyukan Alkhairi da Danlami Kurfi yake yi masu, kuma sunyi godiya da tayashi murna bisa wannan mukami babba a Najeriya da Allah ya bashi. Angudanar da taron na sada zumunci ga ‘yan mazabar ta Barkiya a Dakin taro na HAYATT REGENCY dake bayan ofishin Nigerian Security and Civil Defence a garin Katsina.
Ranar Litinin 29 ga watan Agusta 2023.