Daga Muhammad Kabir
Kamar Yadda Mai Magana Da Yawun Rundunar SP Gambo Isah Ya Fada a Gaban Ƴan Jaridu A Ranar Laraba 31/8/2022 A Jahar Ta Katsina.
Yace “Rundunar Tayi Nasarar Kama Mutane Goma Sha Tara Wadan Da Suka Hada Da Yan Fashi Da Makami Da Fasa Gidajen Mutane Da Bakin Bindiga.
Sana Ya Kara Da Cewa Rundunar Tayi Nasarar Kama Motoci Na Yan Jahar Ta Katsina Wadan Da Aka Sace Samada Guda Goma Sha Ukku.
Isah Ya Kara Da Cewa Rundunar Ta Kama Mutane Bakwai Waɗanda Ake Zargi Da Satar Matar Abdullahi Muhammad Da Mahaifiyar Sa A Karamar Hukumar Danja.
Rundunar Ta Kwato Bindiga Kirar AK 47 Da Harsashi Talatin Da Bakwai A Wani Samame Da Suka Kai Wata Maɓoyar Ƴan Bindiga A Wani Kauye Babban Duhu A Karamar Hukumar Safana.