Hanya na daya daga cikin abinda ke habbaka arziki agari, Inji Masari.

0

Maigirma Gwamnan Jihar Katsina ya fadi hakan ne lokacin da ya kaddamar da fara aikin gina hanya mai nisan kilo mita (25) a garin Kokami dake cikin karamar hukumar Danja, Jihar Katsina .

 

Gwamna Masari yace wannan aikin hanya zai fara daga Garin Danja, Bazanga har zuwa Nahuce da Kokami, haka kuma ya kara da cewa aikin zai lakume zunzurutun kudi kimanin naira Biliyan biyu da miliyan dari hudu.

 

Gwamna Aminu Bello Masari ya cigaba da cewa wannan aiki nada nufin inganta rayuwar al’umma musamman mutanen Karamar Hukumar Danja , domin yin hanyar zai kara haffaka arzikin Karamar hukumar tare da inganta harkar noma, Gwamnan yayi kira ga yan karamar hukumar Danja musamman wadanda zasu amfana da aikin hanyar, da su kula da aikin da kuma bada goyon baya ga masu aikin domin samun nasarar aikin.

 

Haka kuma, Gwamnan ya yi kira ga Kamfanin da zai gudanar da aikin, da ya yi aiki mai nagarta , kuma ya tabbatar da kammala aikin cikin wata (18) kamar yadda aka kulla yarjejeniya da yankwangilar.

 

Daga karshe Gwamna yayi godiya ta musamman ga Babban jagoran shirin na kasa injiniya Aminu Muhammed Bodinga abisa zabar Jihar Katsina acikin wannan shiri .

 

Shima a nashi jawabin, Kwamishinan ma’aikatar kula da muhalli ta Jihar Katsina Hon. Hamza Sule Faskari ya bayyana cewa” za’a gudanar da aikin Karkashin shirin samar da hanyoyi a karkara da bunkasa amfanin gona mai suna yima ( RAAMP).

 

Ya kuma cigaba da bayyana kokarin Gwamnatin Aminu Bello Masari na inganta muhalli a fadin Jihar, na gina magudanan ruwa a fadin Jihar, daga karshe yayi godiya ta musamman abisa irin goyon bayan da Maigirma Gwamna yake ba ma’aikatar wanda wannan ne yasa take samun nasarar gudanar da ayyukanta cikin nasara.

See also  Kai Tsaye: Sakamakon Zaben Gwamna Daga Kananan Hukumomin Jihar Katsina

 

Tun farko da yake gabatar da jawabin maraba, Shugaban shirin na Jihar Katsina Injiniya Falalu Husaini ya bayyana cewa “wannan aiki hanya shi ne na farko a fadin kasar nan karkashin wannan shiri”.

Ya cigaba da cewa “za’a gina hanyar da kwalbatoci, da magudanan ruwa”. ya cigaba da cewa “idan an kammala aikin ana sa ran za ta samar da hanyar shiga yankunan cikin sauki ba tare da wani cikas ba a kowane lokaci da yarda Allah.

 

Dayake jawabin, Shugaban shirin na kasa baki daya Injiniya Aminu Muhammed Bodinga yace “wannan aiki shi ne na farko, amma akwai wasu da dama na nan zuwa. Shima yayi kira ga Al’umma da su bada hadin kai da goyon baya.

Daga karshe yayi godiya ta musamman ga Gwamnatin Maigirma Shugaban Gasa Muhammadu Buhari tare kuma da jinjinama Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari abisa kokarin da yake na ingata rayuwar al’umma. Shima a nashi jawabin Dan Majalisa mai wakiltar karamar hukumar Danja Hon. Shamsuddeen Abubakar Dabai ya godema ma Maigirma Gwamna abisa wannan aiki da aka kawo masu.

 

A nashi jawabin Wakilin Kamfanin na “Mother Cat” da zasu gudanar da aikin, ya yi godiya akan yadda aka ba Kamfanin damar gudanar da wannan aiki tare da yin alkawarin kiyaye yarjejeniyar da aka kulla. Dan haka zasu tabbatar dayin aiki mai kyau kuma mai inganci, zasu Kuma tabbatar da sun kammala aikin cikin watanni (18) kamar yadda akayi yarjejeniya dasu.

 

Daga karshe Shugaban karamar hukumar Danja, Hon. Rabo Tambaya ya yi jawabin godiya tare da fatan alheri ga Gwamnatin Alh Aminu Bello Masari abisa kulawar da Gwamnatin take masu.

 

Daga ofishin Darakta Janar, Sabbin Kafofin Sadarwa na zamani na Maigirma Gwamnan Jihar Katsina.

1/9/2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here