ƳAN BINDIGA SUN KAI HARI GARIN ƊAN-ALHAJI TA BATSARI

0

Misbahu Ahmad

@ katsina city news

 

A daren jumma a 2/9/2022 da misalin 10:00pm wasu gungun ƴan bindiga ɗauke da miyagun makamai sun kai hari garin Ɗan-Alhaji dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari jihar Katsina.

Yan bindigar sunyi ta harbe-harbe kamar zasu tada garin, sannan sun sace dabbobi; tumaki, awaki da shanun garin.

Ƴan bindigar sunyi garkuwa da mutane goma sha shidda, dukkansu mata ne da yara ƙanana.

Koda yake jami’an tsaro sunkai masu ɗauki kamar yadda wani mazaunin garin ya shaida mana.

Zuwan na jami an tsaro ya taimaka wajen rage ta asar yan bindigar.

Jami an tsaron sun fuskance su sosai kuma suka kora su, Wanda ya tsaida ta a sar a garin na Dan Alhaji .

See also  YAN BINDIGA SUN SACE MAI GARIN UMMADAU TA KARAMAR HUKUMAR SAFANA. 

Katsina city news

Www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

Www.jaridartaskarlabarai.com

The links news

@ www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

Email: katsinacitynews2@gmail.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here