ƳAN BINDIGA SUN SAKE TARE HANYAR BATSARI ZUWA KATSINA

0

Misbahu Ahmad

@ katsina city news

Da rana tsaka misalin ƙarfe biyu na rana (02:00PM), jiya jumma a, 2/9/2022, daidai lokacin da masallata ke gabatar da sallar juma’a wasu ƴan bindiga suka tare wata motar fasinjoji, a kusa da garin Taɗeta dake kan hanyar Batsari zuwa Katsina.

Wurin da abun ya faru baifi nisan kilomita daya ba, zuwa inda sansanin sojoji da ƴan banga yake na Batsari.

Majiyar mu ta bayyana cewa sunyi harbe harbe wanda ya kiɗuma mutanen garin

Sannan sunyi nasarar tafiya da direban motar da wasu fasinjoji da bamu iya tantancewa adadin su ba ya zuwa haɗa wannan rahoton.

Katsina city news

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar

@ www.taskarlabarai.com

The links news

@ www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here