AN KAFA CIBIYAR SADARWA TA ZAMANI, DOMIN SAMAR DA TSARO A JIHAR KATSINA.

0

A kokarin ta na ganin bayan ayyukan ta’addanci, da maido da zaman lafiya, Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa cibiyar sadarwa ta zamani, domin karbar korafi da bayar da umarnin gaugawa . Cibiyar wadda take aiki da hadin guiwar dukkan jami’an tsaron da ke aikin samar da tsaro a Jihar Katsina, ita ce irin ta ta farko da aka samar a dukkan fadin jihojin Nigeria.

 

Da yake jawabi lokacin da yake duba kayan aikin da aka samar a cibiyar, Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya jaddada kudurin gwamnatin sa na yin duk mai yuwuwa, domin ganin bayan matsalar tsaro a jihar. Gwamnan ya kara da cewa an kafa cibiyar ne bisa la’akari da muhimmancin sadarwa wurin dakile ayyukan ta’addanci a duk fadin Duniya, daga nan sai ya kalubalanci masu kula da cibiyar da su tabbatar sun samar da wadattatun layukan kar ta kwana, wadan da al’umma za su kira nan take, su shigar da koken kawo masu hari, kuma a kai masu dauki cikin gaugawa.

Duk dai a cikin wannan ziyarar,

Gwamna Masari ya jagoranci sauran shuwagabanni wurin duba yanda wata sabuwar manhajar tsaro, da wani dan asalin jihar Katsina ya samar take aiki, manhajar wadda za ta iya taimakawa mutane su Isar da sako kai tsaye, ga hukumomin tsaro a duk lokacin da barayi ko yanta’adda suka kawo farmaki. Gwamna masari ya yaba wa kwazon matashi dan jihar Katsina Sadiq Jino wanda ya kirkiro wannan manhaja, tare da nuna gamsuwa da yanda take aiki a saukake, musamman da ya kasance cewa duk masu amfani da wayar anduroyid ( Android) za su iya sauke manhajar daga rumbun ajiya na Google Google play store), domin amfana da ita wurin kai rohoton ayyukan ta’addanci, kai tsaye ga cibiyar, domin kawo daukin gaugawa daga jami’an tsaro.

See also  Babbar kotun Tarayya dake katsina tayi Watsi da karar da Sanata Umar kurfi ya shigar

 

A nasa jawabin mai ba gwamna Shawara na musamman kan harkokin tsaro, Alhaji Ibrahim Ahamed Katsina, ya ce cibiyar na aiki ne ta hanyar gudanarwar dukkan hukumomin tsaron da suke aikin samar da zaman lafiya a Jihar Katsina. Ya kara cewa wannan sabuwar manhaja ( security software) da matashi dan jihar Katsina Sadiq Jino ya kirkiro, za ta yi aiki kafada da kafada da wannan cibiya, domin karbar sakonnin wadan da aka kai wa hari daga ko ina a cikin jihar Katsina, da kuma bayar da umarnin kai masu daukin gaugawa domin dakile harin.

 

Daya daga cikin kwararrun da suke jagorancin kula da ayyukan cibiyar, Dr. Mukhtar Alkasim ya fada wa Gwamnan cewa, cibiyar tana sa bangarorin ayyuka guda uku, domin tafiyar da ayyukan sarrafa bayanai cikin sauki . Ya ce akwai sashen gano wurin da ake bukatar kai daukin gaugawa ( Rapid Response Research unit ) sai kuma cikakken sashen bincike ( Full Fledged Research Unit ) sai kuma sashen tattarawa da adana bayanai ( Documentation Unit)

 

Wakilin Hukumar Raya kasa ta majalisar Dinkin Duniya ( UNDP) da ya jagoranci sauran wakilan hukumar, ya jaddada kudurin hukumar na cigaba da tallafa wa gwamanatin jihar Katsina, na ganin ta magance kalubalen tsaro a jihar .

 

Daga Ofishin Darakta Janar mai kula da Sabbin Kafafen Yada Labarai na Gidan Gwamanatin jihar Katsina

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here