Hukumar EFCC ta kama wasu mutane 17 da ake zargi da damfarar Intanet a Benin

0

Jami’an hukumar shiyyar Benin na hukumar EFCC sun kama wasu mutane 17 da ake zargi da damfarar yanar gizo.

An kama su ne a maboyar su da ke cikin garin Benin na jihar Edo biyo bayan bayanan sirri da hukumar ta samu

Hukumar EFCC ta kama wasu mutane 17 da ake zargi da damfarar Intanet a Benin

Wadanda ake zargin su ne Arebu Julius, Ebiechuwa Victory Ovie, John Uwague, Edward Auelimhen, Onyeka Sunday, Omorefe Osazee, Kelvin Emmanuel, Osamuliamen Maxwell, Osrmudiamen Aganjele, Godday Osaretin da Osayande Osariemen. Sauran sun hada da Destiny Enobokhare, Daniel Collins, Collins Edobor, Chukwuemeka Johnson, Omofuma Godpower da Progress Edoagu.

Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu a wurin da aka kama sun hada da wayoyi da kwamfutoci da motoci bakwai na nau’ukan iri daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here