Yadda Wani Mutumin Jigawa Ya Nutse Garin Ceto Shanunsa A Kududufi.

0

Wani matashi dan shekara 18, Adamu Musa na Unguwar Magina, a garin Buji, karamar hukumar Buji na Jihar Jigawa ya rasu a kududufi yayin kokarin ceto shanunsu wacce ta zame ta fada kududufin yayin kiwo.

Kakakin rundunar tsaro ta NSCDC na Jihar Jigawa, CSC Adamu Shehu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Ya ce abin bakin cikin ya faru ne a ranar Asabar misalin karfe 2 na rana lokacin da matashin ya kai shanunsa biyu gona ya sake su suyi kiwo a kusa da gonar.

Ya ce, abin bakin ciki, daya cikin shanun ta zame ta fada cikin kududufi da ke kusa da gonar yayin da suke kiwo.

See also  BUHARI SET TO DISBURSE N300m TO 6,000 SMALL-SCALE FARMERS AND TRADERS IN JIGAWA STATE!

Kakakin hukumar ya ce, ganin abin ya faru, Musa ya garzaya don ceto shanunsa, amma ya nutse, duk da kokarin da mutanen yankin da NSCDC suka yi don ceto shi, ba a gano shi ba sai karfe 1 na yau Lahadi.

majiya: Legit Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here