‘Yan sanda sun kubutar da dan takarar majalisar wakilai na PDP Daga Hannun Yan Bindiga

0

The nation ta ruwaito Cewa A jiya ne jami’an ‘yan sanda a jihar suka kubutar da dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, dan takarar majalisar wakilai a zaben 2023, Ibrahim Tafashiya da wasu da dama da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina a daren ranar Asabar.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, wanda tun da farko ya tabbatar da lamarin ya ce ceton ya biyo bayan matakin da ‘yan sandan suka dauka ne a kan kiran da aka yi musu.

 

Ya ce: “Jami’in ‘yan sanda reshen Kankia Sufeto Ilyasu Ibrahim ne ya jagoranci mutanensa, suka tare ‘yan ta’addan tare da yin artabu da bindiga da ya kai ga ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

 

“Yan ta’addan sun kuma je gidan magatakardar kwalejin ilimi ta Isa Kaita Salisu Gide da ke cikin Garin inda suka yi awon gaba da shi da matarsa.

 

“Bayan samun kira mun yi artabu da ‘yan ta’addan tare da kubutar da shi amma ‘yan ta’addan sun yi nasarar yafiya da matarsa’’.

 

Isah, ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa ana ci gaba da gudanar da wani samame da nufin kubutar da ita da sauran wadan da suke hannun ‘yan ta’addan, saboda an ga ‘yan ta’addan a wani wuri a cikin karamar hukumar Batsari.

 

A halin da ake ciki kuma, an samu makamancin haka da safiyar Lahadi da misalin karfe 5:17 na safe a Sabuwar Kwata da ke karamar hukumar Jibiya inda ‘yan ta’addan suka yi awon gaba da mutane uku da suka hada da yara biyu da wani babba daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here