Ƙungiyar tallafa wa ilimin ƴaƴa mata ta yaba wa Ganduje bisa ɗaukar malamai mata 195 aiki

0

Wata Ƙungiya dake tallafa wa Ilimin ƴaƴa mata, GEP, ta yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa amince wa da ɗaukar malamai mata 195 aiki, ƙarƙashin Ma’aikatar klƘananan Hukumomi.

 

A cikin wata sanarwa da Shugabar ƙungiyar, Hajiya Mairo Bello ta sanya wa hannu a Kano a yau Litinin, ƙungiyar ta kuma nuna matukar godiya ga uwargidan gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje bisa kishin da take da shi na ilimin ƴaƴa mata a jihar.

 

GEP ta yaba da yadda aka ware naira miliyan 100 a cikin kasafin kudin shekarar 2022 domin daukar

 

GEP ta ce ta gamsu da tsarin, inda ta tuna da yadda gwamnatin jihar Kano ta yi amfani da shi a shekarar 2018, Inda ta dauki malamai mata 1,196 wadanda su ke da shedar karatu ta NCE a fadin jihar.

See also  DAME KORAU ZAI NEMI KURI'AR MUTANEN KARAMAR HUKUMAR RIMI

 

Kazalika, ƙungiyar ta nuna gamsuwarta da yadda gwamnati ta raba katon 500 na litattafai da kayan kula da lafiya da tsaftar mata ga makarantun sakandaren mata 15 da ke fadin shiyyoyi guda 3 da ake da su a Kano.

Majiya: daily Nigerian hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here