An Bankado Wasu Dukiyoyin Abba Kyari, An Sake Kai Shi Kotu da Zargin Laifuffuka 24

0

Gwamnatin tarayya ta gano wasu kadarori 14 wanda ake zargin Abba Kyari ya mallaka. Tun tuni dai ake shari’a da babban jami’in ‘dan sandan.

 

Punch ta fitar da rahoto cewa binciken gwamnatin Najeriya ya gano akwai katafaren shaguna, rukunin gidaje da wani filin folo da Abba Kyari ya mallaka.

 

Haka zalika an gano wasu filaye da gidaje a hannun tsohon shugaban na dakarn IRT na kasa.

 

Rahoton yace DCP Kyari bai fadawa hukuma cewa yana da wadannan kadarori a babban birnin tarayya Abuja da garin Maiduguri a jihar Borno ba.

 

Baya ga haka, an samu fiye da Naira miliyan 207 da fam Є17,598 a wasu asusun bankinsa. Darajar wadannan kudi na kasashen waje ya kai N10m.

See also  Ambaliyar Ruwa: Mutum 1 ya mutu, an ceto 4 a Abuja

 

Magana ta je kotu Wannan ya sa Darektan shari’a da gurfanarwa, J. Sunday ya shigar da karar Abba Kyari a kotu a madadin gwamnati, ana tuhumarsa da laifuffuka 24.

 

Ofishin Ministan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin Najeriya yana zargin DCP Kyari da laifin boye gaskiya a game da mallakar wadannan dukiyoyi.

 

An shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CR/408/22 a kotun tarayya na garin Abuja. Mohammed Kyari da Ali Kyari suna cikin wadanda za su amsa laifi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here