Ba ma riƙe makami kuma an hukunta jami’in da ya ɗauki hoto da bindiga – FRSC

0

Hukumar kiyaye Haɗura ta Ƙasa FRSC, ta bayyana cewa jami’anta ba su fara ɗaukar ko wanne nau’in makami ba, walau a yayin sintiri ko kuma a wasu ayyukan na daban.

Shugaban FRSC ɗin na riƙon ƙwarya, Dauda Biu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in fannin wayar da kan jama’a na hukumar, CPEO, FRSC, Bisi Kazeem ya fitar a jiya Lahadi a Abuja.

Biu ya ce bayanan sun yi matukar tasiri ne biyo bayan hoton wani jami’in hukumar da aka ɗauka a hoto ya riƙe bindiga a wani yanayi da ke nuna cewa yana bakin aiki.

“Yakamata a yi watsi da rahoton kwata-kwata domin wani tsohon hoto ne da aka sake yaɗa wa na wani ma’aikacin mu da ya dauki bindigar ma’aikatan hukumar tsaro cikin sha’awa da kuma rashin sanin doka a shekarar 2018.

“An ce tun daga lokacin an hukunta ma’aikatan bisa ga dokar aikin tsaro.

“A halin yanzu jami’anmu ba sa ɗaukar makamai kuma muna ba jama’a shawarar su yi watsi da hoton da ake sake yaɗa wa,” in ji shi.

majiya: Daily Nigeria Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here