Masana sun tabbatar da gano wani abun mamaki a duniyar wata 

0

A karon farko a tarihin duniya, masana ilimin kimiyyar sararin samaniya na kasar Amurka sun tabbatar da gano ruwa da kuma kankara a saman duniyar wata a wani binciken kwana-kwanan nan da suka kammala.

 

Masanan dai sun bayyana cewa wasu wuraren a saman duniyar wata inda rana bata haskawa sanyin wurin yakan kai har ma’aunin yanayin sanyi na digiri Selshios 157.

 

An ce wannan binciken na masana daga kasar Amurka dai na zaman tamkar wani mataki da suka sha alwashi na tabbatar da gano ko za’a iya yin rayuwa a saman duniyar ta wata.

 

Mai karatu dai zai iya tuna cewa tun shekarun baya turawan yamma suke zuwa duniyar watan domin bincike amma sai dai har yanzu babu wanda ya taba zuwa ya dade domin kuwa yanayin duniyar ba zai bari ayi rayuwa ba a cikin ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here